Girgizar Kasa Mai Karfin Gaske Ta Halaka Mutum 632 a Kasar Morocco

Girgizar Kasa Mai Karfin Gaske Ta Halaka Mutum 632 a Kasar Morocco

  • An samu aukuwar iftila'in girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske a yankin birnin Marrakesh na ƙasar Morocco
  • Girgizar wacce ke da ƙarfin maki 6.8 ta auku ne a tsakar daren ranar Juma'a, 8 ga watan Satumban 2023
  • Ma'aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasu ya kai, 632 yayin da wasu mutum 380 suka samu raunika

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Marrakesh, Morocco - An samu girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske a birnin Marrakesh na ƙasar Morocco, a tsakar daren ranar Juma'a, 8 ga watan Satumban 2023.

Mutanen da suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon girgizar ƙasar ya ƙaru zuwa sama da mutum 632, rahoton Sky News ya tabbatar.

Mutum 632 sun mutu a girgizar kasar Morocco
Hukumomi sun tabbatar da cewa mutum 632 sun rasu sakamakon girgizar kasar Hoto: Reuters, NEB Result and News
Asali: Facebook

A cewar bayanai daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar, wasu mutum 329 sun samu raunika, inda mutum 51 ke cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

An Tafka Barna: Kakakin Majalisa Ya Bayyana Asarar Da Najeriya Ta Tafka a Dalilin Satar Man Fetur

Ma’aikatar ta tabbatar da cewa girgizar ƙasar wacce ke da ƙarfin maki 6.8, ta yi ɓarna a yankunan Marrakesh, Al-Haouz, Azilal, Ouarzazate, Taroudant da kuma Chichaoua.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jama'a da dama sun tserewa gidajensu a cikin dare domin kuɓutar da rayukansu, yayin da ake cigaba da aikin ceto, cewar rahoton Aljazeera.

Girgizar ƙasar mai karfi wacce ta auku a Marrakesh, yankin da masu yawon buɗe ido ke yawan zuwa, ta kwashe kusan mintuna 10, sannan an ji motsi a wasu biranen ƙasar da suka haɗa da Rabat, Casablanca da kuma Essaouira.

Ba a taɓa girgizar ƙasa irinta ba a ƙasar

Wakilin jaridar Sky News yana cikin birnin Marrakesh lokacin da iftila'in girgizar ƙasar ya auku a daren na ranar Juma'a.

Ya bayyana cewa girgizar ƙasar ta zarce dukkanin waɗanda ya taɓa gani sun auku a Morocco, inda ba a cika samun iftila'in girgizar ƙasa ba.

Kara karanta wannan

Giro Argungu: Atiku Abubakar Ya Mika Sakon Ta'aziyyarsa Ga Iyalan Malamin

"Tana da ƙarfi sosai, ban taɓa ganin wanu abu makamancinta ba, tana da matuƙar ƙarfi sosai." A cewarsa.

Ya kuma bayyana cewa wasu mutanen sun kwana a tituna saboda tsoron ka da gidajensu su ruguje.

An Samu Girgizar Kasa a Siriya Da Turkiyya

A wani labarin kuma, an sake samun wata sabuwar girgizar kasa da ta auku a iyakar kasashen Turkiyya da Siriya, kwanaki bayan afkuwar ta faro da mutane sama da 40,000 suka kwanta dama a kasashen biyu.

Girgizar kasar mai girman 6.4 ta daki yankin Hatau ne na kasar Turkiyya, wacce ta yi barna a makwanni biyu da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng