Najeriya Ta Yi Asarar $16bn a Dalilin Satar Man Fetur, Tajudeen Abbas

Najeriya Ta Yi Asarar $16bn a Dalilin Satar Man Fetur, Tajudeen Abbas

  • Kakakin majalisar wakilai ya bayyana adadin kuɗaɗen da ƙasar nan ta tafka a dalilin satar man fetur da ake yi
  • Tajudeen Abbas ya bayyana cewa ƙasar nan ta yi asarar $46bn (N16.25trn) a dalilin satar man fetur
  • Kakakin ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da kwamitin majalisar wakilai wanda zai yi bincike kan satar man fetur a ƙasar nan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, a ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba ya bayyana asarar da Najeriya ta tafka a dalilin satar man fetur.

Kakakin ya bayyana cewa ƙasar nan ta yi asarar $46bn (N16.25trn) a dalilin satar man fetur a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2020, cewar rahoton The Nation.

Tajudeen Abbas ya bayyana asarar da kasar nan ta yi a dalilin satar man fetur
Tajudeen ya ce kasar nan ta yi asarar $16bn a dalilin satar man fetur Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Kakakin wanda ya bayyana hakan a wajen ƙaddamar da kwamitin da zai yi bincike kan satar man fetur da raguwar kuɗaɗen shiga daga iskar gas, ya ce satar ta jawo man fetur da ƙasar nan ke samar wa a kowacce rana ya ragu da kaso 5% zuwa 30%.

Kara karanta wannan

Giro Argungu: Atiku Abubakar Ya Mika Sakon Ta'aziyyarsa Ga Iyalan Malamin

Ya nuna kaɗuwarsa kan yadda masu ruwa tsaki a sashen man fetur da iskar gas irinsu NNPCL da sauransu ba su amsa gayyatar da kwamitin binciken ya aike musu da ita ba, rahoton Vanguard ya tabbatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wane abu satar man fetur za ta jawo wa ƙasar nan?

Kakakin wanda ya samu wakilcin, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa idan ba a ɗauki matakin da ya dace ba, ƙasar nan za ta faɗa cikin mummunar matsalar rashin kuɗi saboda raguwar kuɗaden shiga daga sashen man fetur da iskar gas.

Da yake nuni da bayanai daga hukumar Nigeria Extractive Industries Transparency Initiative (NEITI), kakakin ya ce man fetur da ake samar wa ya ragu daga ganga miliyan 2.51 kowacce rana a 2005 zuwa ganga miliyan 1.77 kowacce rana a shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotu: An Bayyana Wani Muhimmin Dalili Da Zai Sanya Shugaba Tinubu Ya Cigaba Da Nasara Akan Atiku Da Peter Obi

"Rahoton NEITI ya nuna cewa an sace man fetur ganga miliyan 619 wanda kuɗinsu ya kai $46bn a tsakanin 2009-2020" A cewarsa.

Farashin Gas Ya Tashi

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa farashin gas ya yi tashin gwauron zaɓi a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke kuka da halin matsin da ake ciki a ƙasa.

Shugaban kungiyar masu siyar da iskar gas (NALPGM), Olatunbosun Oladapo ya bayyana cewa ‘yan kasar za su fara biyan karin kudin gas daga tsakiyar watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel