An samu karamar girgizar kasa a Abuja

An samu karamar girgizar kasa a Abuja

- An samu wata girgizar kasa maras karfi a wasu sassan Abuja

- Sashen bayar da agajin gaggawa na birnin tarayya Abuja (FEMA) ya ce motsawar kasar ta faru a unguwannin Mpape da Maitama a kwaryar birnin Abuja

- FEMA ta ce kada jama'a su tayar da hankalin su tare da bayar da shawarwarin kare kai a lokacin girgizar kasa

A ranar Laraba da yamma ne wasu unguwannin dake cikin kwaryar birnin Abuja suka fuskanci wata girgizar kasa maras karfi.

Biyo bayan karamar girgizar kasar ne, hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin tarayya (FEMA) ta fitar da wata takardar tabbatar da samun rahoton afkuwar hakan tare da bayyana cewar mazauna unguwannin Mpape da Maitama sun sanar dasu batun motsawar kasar.

An samu karamar girgizar kasa a Abuja
Abuja
Asali: Depositphotos

FEMA tayi godiya da kiraye-kirayen da jama'a suka yi domin sanar da su faruwar girgizar kasar tare da zayyana wasu abubuwa dake motsawar kasar.

Hukumar ta ce motsawar wasu duwatsu ko wasu gab'a dake karkashin kasa na daga cikin abubuwan dake haddasa girgizar kasa.

DUBA WANNAN: Osinbajo ya kaddamar da bayar da tallafi ga kananan 'yan kasuwa a kasuwar Abuja, hotuna

FEMA ta shawarci jama'a da kada su damu sannan su bukaci jama'a da su fita daga cikin gidaje ko gini tare da komawa fili da zarar sun ji kasa ta fara girgiza.

Kazalika ta shawarci wadanda ke tafiya a mota da suyi saurin rage gudu tare da neman fili da babu gini ko Bishiya kusa da inda zasu fake har zuwa lokacin da motsin kasar zai tsaya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel