Juyin Mulki: Kungiyar Tarayyar Afrika Ta Dakatar Da Nijar

Juyin Mulki: Kungiyar Tarayyar Afrika Ta Dakatar Da Nijar

  • Ƙungiyar Tarayyar Afrika ta sanar da dakatar da jamhuriyar Nijar daga cikin mambobinta
  • Ƙungiyar ta ce ba za ta mayar da Nijar cikin mambobin na ta ba har sai lokacin da mulki ya bar hannun sojoji
  • Hakan na zuwa ne biyo bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi wa tsohon shugaban ƙasar Mohamed Bazoum

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Adis Ababa, Ethiopia - Kungiyar Tarayyar Afrika (AU), ta sanar da dakatar da jamhuriyar Nijar daga cikin mambobinta, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.

Ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne a yayin taron da ta gudanar ranar Talata, 22 ga watan Agusta a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.

AU ta dakatar da Nijar
Kungiyar Tarayyar Afrika ta dakatar da jamhuriyar Nijar. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Ƙungiyar AU ta dakatar da jamhuriyar Nijar

Matakin dakatarwar da kungiyar ta AU ta ɗauka kan jamhuriyar Nijar na zuwa ne dai a lokacin da ƙungiyar ECOWAS da ma wasu ƙasashe ke ci gaba da sanyawa ƙasar takunkumai daban-daban.

Kara karanta wannan

Aljeriya Na Ba Nijar Wutar Lantarki Kyauta Bayan Najeriya Ta Dai Na Ba Su? Gaskiya Ta Bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ECOWAS dai na ta ƙara gyara tsayuwar a shirin da ta ke yi na ganin ta dawo da mulkin dimokuradiyya hannun Mohamed Bazoum da sojojin suka yi wa juyin mulki.

Ƙungiyar ta Tarayyar Afrika ta ce ba za ta maido da jamhuriyar Nijar cikin mambobinta ba har sai lokacin da mulki ya koma hannun farar hula a ƙasar kamar yadda Channels TV ta wallafa.

AU ta yi gargadi kan katsalandan ɗin ƙasashen wajen nahiyar Afrika

Sai dai ƙungiyar ta AU ta gargaɗi katsalandan ɗin ƙasashen da ba na Afrika ba a cikin rikicin na jamhuriyar Nijar.

Ta kuma ce har yanzu tana kan nazari a kan matakan amfani da ƙarfin soji da ƙungiyar ECOWAS ke shirin yi domin ƙwato mulki hannun sojin Nijar.

ECOWAS dai na ƙoƙarin ganin ta tursasa sojojin juyin mulkin ƙasar su sauka daga mulki tare da mayar da shi hannun hamɓararren shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum.

Kara karanta wannan

Abdourahmane Tchiani Ya Fadi Matakin Da Za Su Dauka Idan ECOWAS Ta Kawowa Nijar Hari

El-Rufai ya gargadi ECOWAS kan amfani da ƙarfin soji a Nijar

Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan martanin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi kan yunƙurin da ƙungiyar ECOWAS take yi na tura dakarun soji Nijar.

El-Rufai ya ce bai kamata Najeriya ta shiga yaƙi da jamhuriyar Nijar ba saboda 'yan uwantaka da ke tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel