Nijar Ba Ta Son Yaki, Amma Za Ta Kare Kanta Daga Hare-Haren ECOWAS, Abdourahmane Tchiani

Nijar Ba Ta Son Yaki, Amma Za Ta Kare Kanta Daga Hare-Haren ECOWAS, Abdourahmane Tchiani

  • Abdourahmane Tchiani, shugaban juyin mulkin Nijar, ya yi martani kan shirin ECOWAS na kai hari
  • Ya ce al'ummar jamhuriyar Nijar ba sa fatan a yi yaƙi, amma za su kare kansu idan hakan ta faru
  • Ya ce sun karɓi mulkin ƙasar ne daga hannun Bazoum ne domin yi wa mutane abinda suke so

Niamey, Nijar - Shugaban juyin mulkin jamhuriyar Nijar, janar Abdourahmane Tchiani, ya yi martani gameda shirin da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), take na kai mu su hari.

Tchiani ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 19 ga watan Agusta kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

Sojojin Nijar sun ce za su kare ƙasarsu daga dukkan hare-hare
Abdourahmane Tchiani ya ce za su kare Nijar idan ECOWAS ta kai ma ta hari. Hoto: ORTN - Télé Sahel/AFP
Asali: Getty Images

Tchiani ya ce Nijar za ta kare kanta daga hare-hare

Abdourahmane Tchiani, ya bayyana cewa ba burin sojojin juyin mulkin ko na 'yan ƙasar ba ne su ga an gwabza yaƙi tsakanin ƙungiyar ta ECOWAS da jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Janar Tchiani Ya Yi Kaca-Kaca Da ECOWAS, Ya Bayyana Matakin Dauka Na Gaba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Tchiani ya bayar da tabbacin cewa za su yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin sun ƙare jamhuriyar ta Nijar idan ya zamto cewa dole sai an gwabza yaƙin.

Ya ƙara da cewa tarin takunkuman da ƙungiyar ta ECOWAS ta sanyawa Nijar suna cutar da al'ummar ƙasar ne kawai, wanda kuma ba hakan ya kamata a yi ba wajen ganin an samu daidaito a tsakani.

Ya kuma ƙara da cewa ba wai sun karɓe ƙasar ba ne kawai don suna son mulki, ya ce sun karɓeta ne domin ganin an yi wa al'ummar ƙasar abinda suke so.

Wakilan ECOWAS sun ziyarci jamhuriyar Nijar

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne dai tawagar wakilci ta ƙungiyar ECOWAS ta ziyarci jamhuriyar Nijar domin tattauna kan yadda za a shawo kan rikicin ƙasar.

Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soji, Abdulsalami Abubakar ne ya jagoranci tawagar, wacce ta haɗa da sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Bayyana Abin Da APC Za Ta Yi Wa Jam’iyyun Adawa a Karkashin Jagorancinsa

Tawagar wakilcin ta samu damar haɗuwa da hamɓararren shugaban na Nijar, Mohamed Bazoum, inda suka tattauna batutuwa da dama da shi kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.

Tchiani ya fadi lokacin da sojojin Nijar za su miƙa mulki ga farar hula

Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan jawabin da shugaban juyin mulkin jamhuriyar Nijar, Abdourahmane Tchiani ya yi wa 'yan ƙasar dangane da lokacin da za su miƙawa farar hula mulki.

Tchiani ya ce ba dadewa za su yi akan mulkin ba, domin kuwa za su shirya sabon zaɓe nan da shekaru uku masu zuwa, amma kafin nan za su fito da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel