Bidiyon Yadda Wani Kamfanin Isra'ila Ya Yi Nasarar Gwajin Mota Mai Tashi Sama Da Yawo A Kasa, Ya Haura N67m

Bidiyon Yadda Wani Kamfanin Isra'ila Ya Yi Nasarar Gwajin Mota Mai Tashi Sama Da Yawo A Kasa, Ya Haura N67m

  • Ana daukan Isra'ilawa a cikin mutane masu basira a duniya saboda fasahar su na iya kere-kere
  • Abin da suka kera a baya-bayan nan shine mota mai tashi a sama, an kuma yi nasarar gwada shi an amince a fara karawa
  • Tuni dai masu hannu da shuni sun fara biyan kudi na motar da za ta shigo gari nan da shekaru biyu

Wani kamfani na Isra'ila mai suna Air One ya yi nasara yin gwajin farko na motarsa na lantarki mai tashi sama kai tsaye da sauka.

Kamfanin a halin yanzu tana shirin fara sayar da motoccin masu tashi sama a karon farko ga al'umma a ƙarshen 2024.

Mota mai tashi sama
Bidiyon Yadda Wani Kamfanin Isra'ila Ya Yi Nasarar Gwajin Mota Mai Tashi Sama Da Yawo A Kasa, Kudinsa Ya Haura N67. Hoto: Credit: AIR/courtesy
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukumar kula da sufurin jiragen sama na kasar ta halarci gwajin motar mai tashi kuma ta bawa kamfanin takardar shaidar gamsuwa.

Kara karanta wannan

Ku Zabe Ni Zaku Samu Tsayayyiyar Wutar Lantarki Ba Tangarda, Inji Tinubu

Yadda motar mai tashi ta ke

Air One mota ce mai aiki da lantarki mai wurin zaman mutum biyu (eVTOL) wacce za ta iya tafiyar nisan kilomita 177 a gudu na kilomita 250 duk awa guda a nisan 1,200 ft, da tafiyan awa ɗaya.

Motar mai tashi, wacce tuni ta samu izinin cancantar tashi a sararin samaniya, tana da fuka-fukai wadanda ke iya boyewa saboda sauƙin fakin, kuma za ta iya tashi sama daga kasa ko wani wuri mai kama da kasa.

An kera motar ne saboda amfani na mutane masu zaman kansu kuma ana fatan zai zama abin biyan bukata ga masu yin gajeruwar tafiya a sama.

Farashin motar mai tashi a sararin samaniya

Shugaban kamfanin Air One kuma daya wadanda suka kafa kamfanin, Rani Plaut cikin wata hira da aka yi da shi ya bayyana cewa tuni mutane 273 sun biya kudinsu na motar Air One, 240 daga cikinsu yan Amurka ne.

Kara karanta wannan

Ya Kamata Ace An Bi Dokar Tsarin Mafi Karancin Albashi Dan Bukasa Kasar Nan, Ministan Buhari

Ya kara da cewa farashin motar mai tashi a sararin samaniya shine $150,000 (N67 miliyan).

Kalamansa:

"Abin farin ciki ne kawo wannan matakin a yunkurin mu na ganin zirga-zirga a sararin samaniya ya zama abu da mutane za su iya yi da kansu.
"Muna sa ran sayar da motocci samu tashi a sama 150 zuwa 200 a shekarar 2024. Hasashen shine sayar da fiye da guda 1000 cikin shekaru biyu, daga nan sai mu kai guda 5000 ko fiye a duk shekara."

Fasihi ya kera mota mai zama jirgi, cikinta tamkar otel

A wani rahoton, wani fasihi mai suna John ya kirkiri wata mota ta musamman, wanda ta ke da kama da jirgin ruwa.

Motar na iya shiga ruwa ta zama kwale-kwale sannan ana iya tafiya da ita a titi lafiya lau kamar sauran motocci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel