Mai fasaha ya kera mota mai zama jirgi, cikinta kamar katafaren otel, har da gidan rawa

Mai fasaha ya kera mota mai zama jirgi, cikinta kamar katafaren otel, har da gidan rawa

  • Wani Bawan Allah mai suna John, mai ‘dan karen hikima, ya kirkiri wata mota mai tattare da gida
  • Bidiyo ya nuna wannan motar tana zama iya kwale-kwale da zarar an tsunbula ta a cikin ruwa
  • Cikin wannan mota da John ya kirkira yana kama da gida, sannan kuma akwai gidan rawa a cikinta

John, wani mutumi mai fasahar gaske, ya kirkiri wata mota ta musamman, wanda take kama da jirgin ruwa.

A wani bidiyo da yake yawo a Facebook, an nuna yadda wannan mota mai ban mamaki take aiki.

Wannan mota ta na iya zama kwale-kwale da zarar ta shiga cikin ruwa. Kuma tana tafiya a titi lafiya kalau.

Idan ta shiga ruwa, bangaren wannan mota yana fitowa, ya bada damar a cigaba da tuka ta tamkar wani jirgi.

Read also

Rikicin VAT: Gwamnatin Buhari na tunanin sasantawa da Wike da Gwamnonin Kudu ta huta

Ba a nan wannan mota ta tsaya ba, za a iya shiryawa ‘dan karamin biki ko ‘yar liyafa a cikin ta

Mutane za su iya holewa a cikin wannan mota-mai-kamar jirgi yayin da take ruwa ko titi, abin gwanin sha’awa.

Mota mai zama jirgin ruwa
Motar Boathome Hoto: Ridiculous ride
Source: Facebook

John ya dade yana burin ya kera motar

Mutumin da ya kera wannan mota, John, ya bayyana cewa ya dade yana burin ya kirkiri wani abu irin wannan.

Da yake bayanin abin da ya sa ya kera wannan mota-jirgi, John yace ya kirkire ta ne domin mutane su ji dadi.

Wannan mota da ake kira boaterhome, ta na duke da wurin dafa abinci, dakin kwana duk abin da ake bukata a gida.

Motar za ta iya zama gidan casu ga masu sha’awar rawa. Kusan duk abin da ake nema a gida, akwai a cikinsa.

Read also

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

Mota mai aiki da lantarki

A kwanakin baya aka ji shugaban hukumar kera motoci a Najeriya (NADDC), Jelani Aliyu, ya fito da wata mota mai amfani da lantarki ta farko da aka kere a Najeriya.

Rahotanni sun ce an yi bikin fito da wannan mota ta kirar 'Hyundai Kano' ne a Fubrairun 2020.

Source: Legit.ng

Online view pixel