Ya Kamata Ace An Bi Dokar Tsarin Mafi Karancin Albashi Dan Bukasa Kasar Nan, Ministan Buhari

Ya Kamata Ace An Bi Dokar Tsarin Mafi Karancin Albashi Dan Bukasa Kasar Nan, Ministan Buhari

  • Batun mafi karancin albashi dai batu ne da ba yau aka fara shi ba, an kusan shafe shekara uku kan batun, amma har yanzu akwai jihohin da basu aiwatar ba
  • Gwamnatin Tarayya ta bullo da tsarin da zai zama albashin da za'a bada mafi karanci shine N33,000 duk wata.
  • Ministan Kwadago da samar da aiyukan yi yace inde za'a aiwatar da tsarin to za'a samu ci gaba a Nigeria sosai da sosai

Abuja: Gwamnatin tarayya tace aiwatar da tsarin biyan mafi karancin albashi abu ne da zai mutukar taimakawa sosai da sosai wajen ci gaban kasa Ake Batun Mafi Karancin, rahoton The Punch

Wannan na kunshe ne cikin jawabin da ministan Kwadago da samar da aikin yi Dr Chris Ngige yayi a wani taron karawa juna sani kan yadda za'a kula da yadda za'a aiwatar da mafi karancin albashi, a Abuja, wanda hukumar kula da albashi da hakokokin ma'aikata ta shirya.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki Ya Gargadi Hukumomin Tsaro Kan Batun Gwamnan CBN

Ngige
Ya Kamata Ace An Bi Dokar Tsarin Mafi Karancin Albashi Dan Bukasa Kasar Nan Ministan Buhari Hoto: UCG
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ministan yace:

"Tabbatar da mafi karancin labashi zai sa a ga canja a wajen ma'aikata."
"Ma'aikacin da yake samu hakkinsa, zaka ga yadda zai rike aikinsa da muhimmanci, wannan kuma shine zai taimaka wajen tafiyar da kasa da ci gabanta
"Akwai bukatar ayi gaggawar aiwatar da tsarin, musamman ma akan ma'aikata da kuma tabbatar da tsarin ya dore dan cin moriyarsa"

Jaridaar NNNews tace shugaban hukumar NSIWC, Ekpo Nta yace hukumar tana duk mai yiwa wajen aiwatar da tsarin, musamman ma a fannin albashi da sauran hakkoki

Yace:

"Hukumar nan zata tabbatar basu samu karanci ko yankewa daga aiwatar da wannan tsarin nan mafi karancin albashi ba"

Akan batun sa ido da bibiya da aka bijiro da shi shekara uku da suka shude, an yi shine dan tabbatar da yadda ake kashe kudaden ma'aikata, inji shugaban hukumar

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Tace Batun Gwamnan Babban Banki Yana Gaban Kotu, Dan Haka Ita Nata Sa Ido

Tun 2019 Ake Batun Mafi Karancin Albashi

Wasu masu fada aji sun yi kira ga gwamnatin tarayya kan ta sanya idanu wajen aiwatar da batun mafi karancin albashi har ma da sauran bukatun ma'aikata, kamar yadda su ka ce wasu hukumomin gwamnatin basa bin dokokin hukumar

Kudirin aiwatar da tsarin mafi karancin albashi dai ba sabon abu bane, tun shekarar 2019 gwamnati ke kokarin aiwatar dashi. duk da akwai jihohin da suka aiwatar kamar Jigawa, Kano da Kaduna, amma har yanzu akwai ma'aikatun gwamnatin tarayya da basu aiwatar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel