Ku Zabe Ni Zaku Samu Tsayayyiyar Wutar Lantarki Ba Tangarda Inji Tinubu

Ku Zabe Ni Zaku Samu Tsayayyiyar Wutar Lantarki Ba Tangarda Inji Tinubu

  • Matsalar wutar lantarki ta zama babbar wata matsala a Nigeria wacce ke kawo nakusu ga ci gaban masa'antun kasar nan
  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmed yace inde 'yan Nigeria suka bashi kuri'a to matsalar tazo karshe
  • 'Yan Nigeria na biyan kudin wutar da suke samu ne ta hanyar amfani da mita ko kuma su biya ta zahiri bisa takardar da aka kawo musu ta adadin wutar da suka sha.

Lagos - Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya ce zai magance matsalar biyan kudin wuta idan aka zabeshi a matsayin shugaban kasa a 2023

Tinubu yayi wannan maganar ne a wajen kaddamar da wani kasuwanci wanda yan kasuwa suka samar mai suna Bussines Forward, jiya Talata a Lagos.

Kara karanta wannan

Muna Rokanka Kaje Ka Huta Karka Yiwa Tinubu Yakin Neman Zabe - PDP Ga Buhari

Jaridar The Cable ta rawaito Tinubun na cewa:

"Ta Kowacce Hanya sai kun samu wuta, a kyauta ba tare da biya kudin wuta ba, idan na zama shugaban kasa, duk wani batu na wuta zai wuce, ku rubuta ku ajiye"

Tinubun yayi alkawarin maida Nigeria wata cibiyar habaka kasuwanci, yana mai cewa zai cire tallafin man fetir sabida Nigeria bazata ci gaba da baiwa wata kasa arzikinta ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu
Ku Zabe Ni Zaku Samu Tsayayyiyar Wutar Lantarki Ba Tangarda Inji Tinubu Hoto: The Cable
Asali: UGC

Ya ce:

"Ya zamu ringa bada tallafin mai ga kasar Camerron ko Niger Ko Benin, duk halin da aka shiga kamata yayi ace mun cire tallafin fetir sai muyi amfani dashi wajen bunkasa fannin ilimin mu."

Tsohon gwamnan ya ce gwamnatinsa zata bawa bangarori wanda bana gwamnati ba dama, zasu sakar musu mara wajen gudanar da aiyukansu.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki Ya Gargadi Hukumomin Tsaro Kan Batun Gwamnan CBN

Jaridar NairaLand ta rawaito cewa tinubu yayi alakawarin samar da wutar lantarki awa ashirin da hudu tsawon kwana bakwai muddin aka zabeshi. Tinubun na fadin hakan ne ta hannun mai taimaka masa kan kafafen sadarwa, a ranar 22 ga watan Mayun wannan shekarar

Zan Bunkasa Kasuwanci Sosai In Aka Zabe Ni

Tinubu yace idan aka zabe shi zai hada hannu da 'yan kasuwa wajen da kungiyoyi ko bangarorin da ba na gwamnati ba wajen bunkasa harkokin kasuwanci, da habaka samar da abubuwan da 'yan Nigeria ke bukata.

Tinubu yace Burina na shi ne mu inganta harkokin mu da muke yi da kanmu, wajen habaka masa'antun mu na gida, wanda kuma zamu ringa iya fitar da su sauran kasashen duniya, domin su ga abinda muma mukeyi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel