Jami'a A Uganda Ta Umurci Ɗalibai Su Yi Gwajin Juna Biyu Kafin Rubuta Jarrabawarsu Ta Ƙarshe

Jami'a A Uganda Ta Umurci Ɗalibai Su Yi Gwajin Juna Biyu Kafin Rubuta Jarrabawarsu Ta Ƙarshe

  • Wata jami'a mai suna 'Kampala International University' a kasar Uganda ta umurci dalibai mata su yi gwajin juna biyu kafin rubuta jarrabawa
  • Wannan umurnin ya janyo suka daga majalisar kasar da kuma masu rajin kare hakkin mata a dandalin sada zumunta
  • Ba tare da bada dalilin umurnin ba, jami'ar daga baya ta janye umurnin ta kuma yi wa daliban fatan alheri a jarrabawarsu

Uganda - Wata jami'a mai zaman kanta a Uganda ta janyo cece-kuce a ranar Alhamis bayan ta fada wa wasu dalibai mata cewa sai an musu gwajin juna biyu kafin za su rubuta jarrabawar karshe, Daily Trust ta rahoto.

Umurnin na Jami'ar Kasa da Kasa ta Kampala - da aka bayyana a matsayin "abin nuna wariya da ba za a amince da shi ba' an janye shi biyo bayan shan suka.

Kara karanta wannan

Sai dai Mu Tafi Lahira da Yawa: Jinina Nake Gaurayawa da Zobon Siyarwa, Mai Kanjamau

Gwajin Juna Biyu
Jami'a A Uganda Ta Umurci Dalibai Suyi Gwajin Juna Biyu Kafin Rubuta Jarrabawa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani sanarwa na cikin jami'ar da AFP ta samu a ranar Alhamis ya umurci dukkan dalibai masu karatun ma'aiktan jinya da unguwar zoma su yi gwajin juna biyu kan kudi shilling 5,000 na Uganda ($1.30).

Ta ce:

"Idan ba a yi hakan ba, ba za ku rubuta jarrabawar UNMEB (Hukumar kula da ma'aikatan jinya da unguwar zoma) ba."

Kakakin majalisar Uganda ta soki umurnin

An tattauna batun a majalisa a ranar Alhamis, inda kakakin majalisar Anita Among ta bayyana umurnin a matsayin 'abin takaici' tana mai cewa dalibai masu juna biyu suna da damar rubuta jarrabawar.

MP Sarah ta yi kira ga majalisar ta tabbatar babu wata jami'ar da ta sake bada irin wannan umurnin.

Mai rajin kare hakkin mata Catherine Kyobutungi a Twitter ta ce:

"Wannan shirme ne baki daya, nuna wariya ne kuma abin da ba za a yarda da shi ba."

Kara karanta wannan

Jama’a Sun Yi wa Sarki Charles III da Matarsa Ihun Bama so tare da Jifansu da Kwai a Ingila

Jami'ar ta janye umurnin

Frank Kaharuza Mugisha, mataimakin shugaban jam'ar inda daliban aikin jinya da unguwar zoma suke, daga baya ya sanar an janye umurnin, rahoton The Star.

A cikin wata takarda ya da fitar, ba tare da bata dalilan umurnin na farko ba ya ce:

"Don Allah ku mayar da hankali wurin shirin rubuta jarrabawar ku. Ina muku fatan alheri a jarrabawar da ke tafe."

Babbar Yarinya Ta Yi Kudin Jirgi Daga Landan Domin Dawowa Najeriya Saboda an Janye Yajin ASUU

Wata babbar yarinya 'yar Najeriya ta hau jirgin sama daga birnin Landan zuwa Najeriya jim kadan bayan ASUU ta janye yajin aiki a kasar.

Budurwar mai suna @mimii_chi a kafar TikTok ta yada yadda tafiyarta ta kasance a wani bidiyon da ta fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel