Sarki Charles III da Matarsa Sun Sha da Kyar Bayan An Jefe Su

Sarki Charles III da Matarsa Sun Sha da Kyar Bayan An Jefe Su

  • Wani mai rajin kare hakkin ‘dan Adam ya jefa Sarki Charles III da matarsa sarauniya Camilla da kwayaye uku amma bai same su ba ya fadi kasa
  • Tuni jami’an tsaro suka hanzarta cafke wanda ake zargin yayin da yake ihun fadin an gina kasar da jinin bayi ne ba da adalci ba
  • Barasaken da matarsa sun halarci birnin arewacin Ingilan ne domin halarta bude gunkin marigayiya Elizabeth ta II, na farko bayan mutuwarta

Sarki Charles III da matarsa Sarauniya Camilla sun sha da kyar yayin da aka jefe su da kwai yayin da suka ziyarci arewacin Ingila a ranar Laraba, kafar yada labaran Birtaniya ya bayyana hakan, Channels TV ta rahoto.

Sarki Charles III
Sarki Charles III da Matarsa Sun Sha da Kyar Bayan An Jefe Su. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Basaraken mai shekaru 73 da matarsa Camilla mai shekaru 75 an so jifan su da kwayaye uku wadanda suka fada kusa da su yayin da suke tafe a York kafin su wuce.

Kara karanta wannan

Abin ya fara yawa: Ni da Masoyana Na Fuskantar Hadari Daga APC - Atiku Ya Koka

Jami’an tsaro sun kama wanda ake zargin

An ji wani mutumi yana ihun cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wannan kasar an gina ta ne da jinin bayi kuma kai ba sarki na bane,”

Kafin jami’an ‘yan sanda su kama shi kamar yadda bidiyon ya nuna.

Masu zanga-zangar sun dinga yi wa basaraken da matarsa ihun bama yi kafin a jefe su da kwai kamar yadda ‘yan jarida suka bayyana.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, sauran jama’a da suka taru a Micklegate Bar domin ziyarar an ji suna cewa:

“Allah ya tsare Sarki, Kun ji kunya.”

Ga masu zanga-zangar.

Dalilin ziyarar sarkin

Charles da Camilla sun cigaba da ziyartar al’adar yayin da ‘yan sanda suka kwashe wadanda ake zargin.

Kafafen yada labaran Ingila sun bayyana shi a matsayin tsohon ‘dan takarar jam’iyyar Green kuma mai rajin kare hakkin ‘dan Adam da kungiyar ‘yan tawaye.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Hargitsa Kauye, Sun Yi Awon Gaba da Basarake da Mutanen Gari

Jinin sarautar sun halarci birnin ne domin halartar bude gunkin tsohuwar sarauniya Elizabeth II, na farko da aka fara kafawa tun bayan mutuwarta a ranar 8 ga watan Satumban 2022.

Sarauniyar ta kafa tarihin zama basarakiyar da tafi dadewa a kujerar sarautar Ingila a tarihi amma ta rasa ranta a ranar 8 ga watan Satumban 2022.

Babu bata lokaci babban ‘dan sarauniyar mai shekaru 73 ya maye gurbinta inda ya zama sabon sarkin Ingila duk da sai shekara mai zuwa za a yi shagalin nadin sarauta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel