Babbar Yarinya Ta Yi Kudin Jirgi Daga Landan Domin Dawowa Najeriya Saboda an Janye Yajin ASUU

Babbar Yarinya Ta Yi Kudin Jirgi Daga Landan Domin Dawowa Najeriya Saboda an Janye Yajin ASUU

  • Kungiyar malaman jami'o'i a Najeriya (ASUU) ta janye yajin aiki, don haka wata daliba 'yar Najeriya ta hau jirgi daga Landan domin ta dawo gida Najeriya
  • Budurwar ta yada wani bidiyon lokacin da take cikin jirgi a shirinta na dawowa gida domin ci gaba da karatun jami'a
  • Jama'a da dama sun yi mamaki, wannan yasa da dama suka yi ta magana kan wannan yunkuri nata mai ban mamaki

Wata babbar yarinya 'yar Najeriya ta hau jirgi daga birnin Landan zuwa Najeriya jim kadan bayan da ASUU ta janye yajin aiki a kasar.

Budurwar mai suna @mimii_chi a kafar TikTok ta yada yadda tafiyarta ta kasance a wani bidiyon da ta sake.

A bidiyon, an ga budurwar a jirgi, lamarin da ya ba wasu mutane da dama mamaki ganin tana zaune a kasar waje amma ta dawo Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnati ba za ta iya rike jami'o'i ba, ya kamata iyaye su fara kawo tallafi, inji gwamnan APC

Budurwar da ta taso daga Landan don zuwa karatu Najeriya
Babbar yarinya ta yi kudin jirgi daga Landan domin dawowa Najeriya saboda an janye yajin ASUU | Hoto: @mimii_chi
Asali: UGC

Ta kuma nuna lokacin da take dakon jakunkunanta a filin jirgin dake nuna alamar da gaske tafiyar take.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

ASUU ta janye yajin aiki

Budurwar ta dago wannan tafiyan ne jim kadan bayan da ASUU ta sanar da janye yajin aikin da ta shiga tun watan Fabrairu.

Kungiyar malaman jami'a ta shafe watanni sama da takwas ba tare da koyar da daliban jami'o'i ba saboda rikicin dake tsakaninsu da gwamnati.

Akwai yiwuwar wannan budurwar ta shafe lokaci ne a turai saboda yajin aikin da kungiyar ke, duk da dai Legit.ng bata tabbatar ba.

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan TikTok

Jama'ar TikTok sun yi martani ga wannan budurwa, ga dai abin da suke fadi:

@Non So336 yace:

"Har ma kina iya zuwa hutu kasar waje, 'ya'yan masu kudi kenan."

@Sterling.gray yace:

"Ta dai daura ne kaiwa, ba zan yarda cewa ta dawo gida bane."

Kara karanta wannan

Karshen yajin aiki: ASUU za ta shiga tattaunawar karshe kan warware yajin aiki

@Gina Godwin yace:

"'Yar uwata ki yi karatunki a can fa, wannan dai ya zama hutu kawai."

@Kelly Mbaka yce:

"Idan wani zafi ya dumfare ki bayan sauka daga jirgi sannan kika ji wata gaisuwa daga jami'in tsaro 'me zan samu ne' za ki gane."

@praise dyna yace:

"Ni da nake dawowa kullum makwanni uku bayan dawowa."

@Omo.zoba yace

"Da sauri-sauri."

Gwamnatin Tarayya Kadai Ba Za Ta Iya Rike Jami'o'i Ba, Iyaye Ya Kamata Su Fara Tallafawa, Inji Gwamna Inuwa

A wani labarin, gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya kadai ba ta da karfin iya rike jami'o'in kasar, Channels Tv ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar iyaye da sauran masu ruwa da tsaki suke shiga lamarin domin tabbatar da tafiyar da makarantu cikin kwanciyar hankali.

Gwamnan ya bayyana hakan a ranar Juma'a jim kadan bayan da kungiyar ASUU ta ayyana janye yajin aikin da ta shafe watanni takwasi tana yi a kasar.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da aka ga bidiyon mata mai juna biyu na leburanci a wurin wani gini

Asali: Legit.ng

Online view pixel