Ba Zan Mutu Ni Daya ba: Yadda Mai Kanjamau Ke Gauraya Jininta da Zobon Siyarwa

Ba Zan Mutu Ni Daya ba: Yadda Mai Kanjamau Ke Gauraya Jininta da Zobon Siyarwa

  • Mata mai cutar kanjamau ta bayyana yadda take zukar jininta tana gaurayawa da zobon da take siyarwa inda take kai shi kasuwa ana siya
  • Kamar yadda ta sanar a wani kiran da tayi yayin shirin gidan rediyo, ta samu cutar watanni 6 da suka gabata kuma bata so ta mutu ita kadai
  • Ta sanar da cewa, da sirinji take zukar jinin nata sannan ta zuba a zobo, bata alfahari da abinda take amma tana farin ciki ba ita daya zata mutu ba

Wata mata wacce har yanzu ba a gano ta ba, mai dauke da cutar kanjamau tace tana hada jininta a cikin zobo da take yi na siyarwa domin ta samu shafawa jama’a cutar mai karya garkuwar jiki.

Zobo drink
Ba Zan Mutu Ni Daya ba: Yadda Mai Kanjamau Ke Gauraya Jininta da Zobon Siyarwa. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Matar dai ta bayyana wannan mugunta da tayi ne a wani shirin gidan rediyon Wazobia mai suna MarketRunz wanda ake yi a daren Laraba, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jama’a Sun Yi wa Sarki Charles III da Matarsa Ihun Bama so tare da Jifansu da Kwai a Ingila

Mai gabatar da shirin ya bukaci ji daga bakin masu sauraro dake kira kan abinda suke yi a kasuwa wanda jama’a ba su sani ba kuma ba zasu so ya fallasu ba, Daily Trust ta rahoto.

Zobo mai kanjamau ke siyarwa

Mai siyar da zobon tace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Naje asibiti watanni shida da suka gabata kuma an sanar min cewa ina dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.
“Bani da kudin magani don haka na yanke hukuncin cewa ba zan mutu ni kadai ba. Na fara hada zobo na sa jinina kuma ina hadawa tare da siyarwa jama’a.
“Da sirinji nake zukar jinina kuma ina hada da zobon. Ni ma’aikaciyar jinya ce da farko amma da na samu kanjamau dole na bar aikin.
“Bana alfahari da abinda nake yi amma ina farin cikin cewa ba ni kadai zan mutu ba.

Kara karanta wannan

Ina Addu’a Kada Allah ya Bani Haihuwa, Yara Dawainiya ne: Budurwa a Bidiyo

“Yanzu wata na shida ina yin hakan kuma ina fatan Ubangiji ya yafe min.”

Jama’a kan yi kyamar masu siyar da abubuwan ci da sha idan basu da tsafta

Mutane masu tarin yawa kan yi kyamar masu sana’ar abin ci ko sha idan tsaftarsu tayi karanci.

Sau da yawa jama’a kan guji irin wadannan masu abincin siyarwan ne domin gudun daukar cut kamar amai da gudawa da sauransu.

Tunanin jama’a ba zai taba kai wa har kan kanjamau ba ganin cewa haduwar jini ce ke kawo shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel