Abin Mamaki Yayin Da Masu Jefa Ƙuria Na Amurka Suka Sake Zaɓen Mataccen Ɗan Majalisa A Zaɓen Tsakiyar Zango

Abin Mamaki Yayin Da Masu Jefa Ƙuria Na Amurka Suka Sake Zaɓen Mataccen Ɗan Majalisa A Zaɓen Tsakiyar Zango

  • Wani labari da zai ya bawa wasu tsoro amma ya kayatar da wasu shine sake zaben dan jam'iyyar Democrat, Tony DeLuca, dan majalisar Pennsylvania a Amurka
  • Yayin zabukan tsakiyar zango, masu zabe a Amurka a ranar Talata 8 ga watan Nuwamba, sun sake zaben dan siyasan da ya rasu a watan Oktoba da ya gabata
  • Wannan matakin ya sa za a sake yin wani zabe a nan gaba don cike gurbin da marigayin ya bari

Amurka - Dan jam'iyyar Democrat, Tony DeLuca, dan majalisa mai wakiltar jihar Pennsylvania a Amurka wanda ya mutu a watan da ya gabata, 'ya sake cin zabe' yayin zabukan tsakiyar zango, Daily Trust ta rahoto.

DeLuca ya rasu a ranar 9 ga watan Oktoba, bayan fama da ciwon lymphoma, cutar da sau biyu yana kamuwa amma ya warke. Ya rasu yana da shekaru 85 a duniya, rahoton Independent.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Abin Fashewa Ya Yi Mummunar Ɓarna A Babban Kasuwa A Najeriya

DeLuca
Zaɓen Tsakiyar Zango: Abin Mamaki Yayin Da Masu Jefa ƙuria Na Amurka Suka Sake Zaɓen Mataccen Dan Majalisa. Hoto: CNN
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fox News ta ambato Pittsburgh Post-Gazette na cewa shine dan majalisa wanda ya fi dadewa kan kujerarsa a jihar Pennslyvania.

A wani rubutu a Twitter, yan Democrat na Pennsylvania sun ce:

"Mun yi matukar bakin cikin rasa Dan Majalisa Tony DeLuca, mun yi alfaharin ganin yadda masu zabe suka fito suka nuna gamsuwarsu da shi da akidun Demokradiyya ta hanyar sake zabensa duk da ya rasu. Za a yi zabe na musamman nan gaba."

Wasu masu nazarin al'amura sun yi hasashen cewa masu jefa kuri'a sun zabi DeLuca ne duk da cewa sun san ya rasu saboda su tursasa yin zabe na musamman a maimakon zaben abokin hammayarsa, a cewar dan jarida a garin, Charlie Wolfson.

Abokiyar hammayar DeLuca

Abokiyar hamayyar DeLuca, Queonia Livingston, ta yi takara, inda ta sanya muhimman abubuwa uku a shafinta na yanar gizo kamar haka; adalci na muhalli, kawo karshen yakin da ake yi da kwayoyi da kuma rage tashin hankalin bindiga.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Fitaccen dan takarar majalisar wakilai a APC ya yi hadari, ya rasu

A kalla yan siyasa yan asalin Najeriya guda takwas ne suka ci zabe a zabukan tsakiyar zango da ake yi a Amurka a halin yanzu.

Zaben Amurka: Cikakken Jerin 'Yan Najeriya Da Suka Ci Kujerun 'Yan Majalisu A Georgia, Pennsylvania, Minnesota

A wani rahoton, kimanin yan siyasa 8 yan asalin Najeriya a Amurka ne suka yi nasarar lashe zabukan majalisu a jihohin Georgia, Pennsylvania da Minnesota.

A cewar Sahara Reporters, shugaban hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta tabbatar da hakan a sahihin shafinta na Twitter.

Asali: Legit.ng

Online view pixel