Zaben Amurka: Cikakken Jerin 'Yan Najeriya Da Suka Ci Kujerun 'Yan Majalisu A Georgia, Pennsylvania, Minnesota

Zaben Amurka: Cikakken Jerin 'Yan Najeriya Da Suka Ci Kujerun 'Yan Majalisu A Georgia, Pennsylvania, Minnesota

  • A kalla yan asalin Najeriya guda 8 ne suka lashe kujerun majalisa a jihohin Georgia, Pennsylvania da Minnesota a Amurka
  • Solomon Adesanya da Tish Naghise na cikin Amurkawa yan asalin Najeriya da za su rika yin dokoki a Amurka
  • Abike Dabiri-Erewa, shugaban hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, wacce ta wallafa labarin a shafinta na Twitter, ta taya su murna a madadin gwamnatin tarayya

Amurka - Kimanin yan siyasa 8 yan asalin Najeriya a Amurka ne suka yi nasarar lashe zabukan majalisu a jihohin Georgia, Pennsylvania da Minnesota.

A cewar Sahara Reporters, shugaban hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta tabbatar da hakan a sahihin shafinta na Twitter.

Yan siyasan Najeriya a Amurka
Zaben Amurka: Cikakkun Jerin 'Yan Najeriya Da Suka Ci Kujerun 'Yan Majalisu A Georgia, Pennsylvania, Minnesota. Hoto: Abike Dabiri-Erewa
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Diyar Tsohon Shugaban Kasan Amurka Zata Auri ‘Dan Najeriya, Shagulgula Sun Kankama

Yan Najeriya da ke Amurka a zaben Amurka

An zabi yan Najeriya matsayin yan majalisu a ranar Talata, 8 ga watan Nuwamba, a yayin da Dabiri-Erewa ta aike musu da sakon taya murna.

Abike Dabiri-Erewa ta ce:

"Wadannan Amurkawan yan Najeriyan sun ci zabensu a Georgia a daren jiya. Ina taya su murna baki daya. #ProudlyNigerian."

Ga jerin sunan yan Najeriyan a kasa:

  1. Segun Adeyina
  2. Gabe Okoye
  3. Solomon Adesanya
  4. Tish Naghise
  5. Phil Olaleye
  6. Carol Kazeem
  7. Oye Owolewa
  8. Esther Agbaje

Akwai wasu zabukan da za a sake yin zaben raba gardama cikin zabukan da aka yi a ranar Talata 8 ga watan Nuwamban, amma ba a bayyana ranar yi ba.

Zaben 2023: Jam’iyyar PDP ta Bayyana Shirinta Na Hambarar Da APC A Wani Babban Jihar Arewa

A bangare guda, babban jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta ce za ta yi kamfen din dan takarar shugaban kasarta a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamban 2022 a Maiduguri, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Lalong Ya Shigar Da Ali Nuhu, Duniyar Kannywood Yakin Neman Zaben Tinubu/Shettima

Jam'iyyar na cike da kwarin gwiwa tana mai cewa dan takarar shugaban kasarta, Atiku Abubakar zai ci galaba a Borno a babban zaben 2023 da ke tafe, Channels TV ta rahoto.

Mai magana da yawun PDP, Debo Ologunagba cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai ya yi ikirarin Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ba shi ga magoya baya sosai a jihar Borno duk da cewa jihar na karkashin jam'iyyar APC ne kuma jihar abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel