Wani Abin Fashewa Ya Yi Mummunar Ɓarna A Babban Kasuwa A Najeriya

Wani Abin Fashewa Ya Yi Mummunar Ɓarna A Babban Kasuwa A Najeriya

  • An tafka asarar kayayyakin da aka kiyasta sun kai biliyan daya a gobarar da ta tashi a kasuwar kemikal ta Onitsha
  • Shaidan gani da ido ya bayyana cewa suna zaune a ranar Talata ne kwatsam suka ji kara mai karfi sannan suka hangi hayaki ya turneki a wasu shaguna da ke bene
  • DSP Ikenga Tochukwu, mai magana da yawun yan sandan jihar Anambra ya ce babu wanda ya rasu sakamakon gobarar akasin abin da shaidan gani da ido ya fada

Onitsha - An rahoto cewa mutane hudu sun rasu a ranar Talata yayin da da dama sun yi munanan rauni bayan abin fashewa ya fashe a kasuwar Kemikal ta Onitsha Head Bridge, Jihar Anambra.

A cewar shaidun gani da ido, an ciro gawarwarkin wadanda suka rasu daga kasuwar, yayin da ake ceto wadanda suka yi rauni, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Fitaccen dan takarar majalisar wakilai a APC ya yi hadari, ya rasu

Kasuwar Onitsa
Wani Abin Fashewa Ya Yi Mummunar Barna A Kasuwar Onitsha. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kayayyaki na miliyoyin naira sun salwanta sakamakon wutan da ta kona shaguna.

An tattaro cewa wutan ta fara ci ne misalin karfe 12.10 na ranar Talata a yayin da kemikal da aka ajiye suka fashewa, rahoton Vanguard.

Jami'an hukumar kwana-kwana na jihar Anambra da Delta sun isa wurin don kashe gobarar.

Ba a rasa rayyuka ba - Kakakin yan sanda, DSP Ikenga Tochukwu

Kakakin yan sandan Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce babu wanda ya mutu amma abin da shaidan gani da ido ya fada ya sha banban da hakan.

A cewar shaidan gani da idon, shugaban karamar hukumar Onitsha ta Kudu, Mr Emeka Orji, ya garzaya wurin da abin ya faru bayan samun labari.

Shaidan gani da ido ya ce an rasa rayyuka

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

Daya daga cikin yan kasuwar, Mr Nweke Uchenna, ya shaidawa Daily Trust cewa:

"Muna shagonmu kamar yadda muka saba sai muka ji kara tambar ta bam kuma muka ga hayaki na fitowa daga shaguna da ke bene sai kowa ya fara gudu. Sai mutane suka fara ihun neman taimako kuma mun ga ana ciro mutane daga shagunan da suka kamata da wuta. Wasu na da rai amma sun kone sosai; yayin da wasu tamkar hayaki da turareniya yasa sun dena numfashi.
"Ba mu san ko nawa aka rasa ba amma ana iya kiyasin wutar ya kone dukiyar Naira miliyan 850 zuwa Naira biliyan 1 saboda kayan kemikal suna da saurin konewa."

Ga hotunan abin da ya faru a kasuwar daga kasa:

Gobarar Kasuwar Onitsha
Motar kashe gobara tare da mutane suna bada taimako a kasuwar Onitsha. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Gobarar kasuwar Onitsha
Jami'an kwana-kwana da mutane na kokarin kashe wuta a kasuwar Onitsha. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Wani abin fashewa ya tashi da daliban makaranta a jihar Kano

Rahotanni sun nuna cewa wani abin fashewa ya tashi a jihar Kano, arewa maso yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Manoma sun huta, sojoji sun sheke wani kasurgumin shugaban 'yan bindiga a Zamfara

BBC Hausa ya rahoto cewa abin ya tashi a Aba Road da Sabon Gari a birnin Kano.

Nafi'u Nuhu Indabo, shugaban kasuwar Sabon Gari ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa ya rutsa da mutane da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel