Bidiyon Da Hotunan Yadda Sabuwar Gada Ta Rufta Da Jami'an Gwamnati Yayin Bikin Kaddamarwa a DRC

Bidiyon Da Hotunan Yadda Sabuwar Gada Ta Rufta Da Jami'an Gwamnati Yayin Bikin Kaddamarwa a DRC

  • Wata sabuwar gada da aka gina ta Jamhuriyar Demokradiyya ta Congo, DRC, ta rufta yayin bikin kaddamarwa a DRC
  • Bidiyon bikin kaddamarwar ya nuna jami'an gwamnati tare da mutane sun hau gadan yayin da wasu suke kasa suna kallo
  • A lokacin da jami'in gwamnati ya karba almakashi zai datse ribon na kaddamarwa kawai sai gadar ta rufta wasu suka fada kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

DRC - Hankula sun tashi bayan wani karamin gada tsallakawa da kafa ya rufta a lokacin bikin kaddamar da shi a Jamhuriyar Demokradiyya ta Congo, (DRC).

Yan siyasa na Africa sun yi kaurin suna wurin yin manyan bukukuwa yayin kaddamar da ayyuka da suka yi.

A shekarar 2018, tsohon ministan kudi na Zimbabewa Patrick Chinamasa ya kaddamar da kwandon zuba shara kuma labarin ya bazu sosai a lokacin.

Kara karanta wannan

Zaman Dubai Sai An Shirya: Bidiyon Wasu Karatan Maza Suna Aikin Wanke-Wanke Don Samun Na Kashewa

Kaddamar da gada a DRC
Bidiyon Da Hotunan Yadda Gada Ta Rufa Da Jami'an Gwamnati Yayin Kaddamarwa. Hoto: Harare
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan karon, yan siyasa ne daga kasar ta DRC suka so kaddamar da karamar gada na takawa da kafa, sai dai abubuwa ba su tafi yadda aka tsara ba.

Jami'an gwamnati sun taru don bikin. An gina karamin gadan ne don taimaka wa mutane tsallaka rafi a lokacin damina, don ruwa na shanye tsohuwar gadar.

Wasu mutane sun hau kan gadar, wanda fadinsa bai wuce mita biyu ba. A karshensa, an lika ribon mai launin ja, da ake sa ran daya cikin jami'an zai yanka da almakashi.

Kaddamar da gada a DRC.
Bidiyon Da Hotunan Yadda Gada Ta Rufa Da Jami'an Gwamnati Yayin Kaddamarwa. Hoto: Harare.
Asali: Facebook

Kaddamar da gada a DRC
Bidiyon Da Hotunan Yadda Gada Ta Rufa Da Jami'an Gwamnati Yayin Kaddamarwa. Hoto: Harare.
Asali: UGC

Kamar yadda bidiyon ya nuna, a lokacin da suke kan gadar, wasu tawagar mutanen suna kasa suna kalon bikin kaddamarwar.

Yadda sabuwar gadan ta rufta da jami'an gwamnatin DRC

Nauyi ya yi wa gadar yawa lokacin da ake yanke ribon din, kuma ta rufta ta rabe biyu a yayin da mutane ke kan gadar.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

A lokacin ne abubuwa suke rikice.

Matar da ke rike da almakashin ta yi kokarin tsalle ta dira amma wani mutum mai girman jiki da ke kusa da ita ya tare ta da gwiwan hannunsa don shima kada ya fadi.

Ta rike mutumin sosai, a yayin da jami'an tsaro suka garzayo suka rike ta kada ta fada kasa. Wanda ke bayan matar ya riko ta, sauran mutanen da ke baya suka tsaya charko-charko, wadanda kuma ba su yi sa'a ba suka fada kasa.

2023: Ku Tashi Ku 'Ƙwace' Mulki Daga Hannun Dattijai, Gwamna Ya Zaburar Da Matasan Nigeria

A wani labari daban, Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi ya ce matasan Nigeria ba su nuna wa dattijai cewa 'lallai da gaske suke son karɓe shugabancin kasa ba', rahoton The Cable.

Bello, wanda tuni ya bayyana niyyarsa na yin takarar shugabancin kasa, a ranar Talata ya yi kira ga matasa su yi aiki don ganin sun 'ƙarbe' mulki daga hannun dattawa gabanin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Akan N1,500 na kudin wutan lantarki, wani ya bindige kaninsa har lahira

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a Ijebu-Ode, jihar Ogun, a wurin wani taro da aka yi wa laƙabin: "Matasa ke da iko a hannun su'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel