Zaman Dubai Sai An Shirya: Bidiyon Wasu Karatan Maza Suna Aikin Wanke-Wanke Don Samun Na Kashewa

Zaman Dubai Sai An Shirya: Bidiyon Wasu Karatan Maza Suna Aikin Wanke-Wanke Don Samun Na Kashewa

  • Wata matashiya ta yada bidiyon wasu maza bakaken fata a kasar Dubai suna aikin wanke-wanke lamarin da ya baiwa mutane mamaki
  • An gano tulin kwanuka, kofuna da cokula masu datti kewaye da su yayin da suke gudanar da aikinsu cikin azama
  • Yayin da wasu mabiya soshiyal midiya ke cewa ba za su taba yin irin wannan aikin ba, wasu sun ce ana biyansu albashi mai tsoka

Dubai - Wani dan gajeren bidiyo da aka wallafa a TikTok ya nuna cewa mutane da dama da ke zuwa kasar waje don aiki suna shan fama don tara kudade, suna yin harda da irin ayyukan da ba za su iya yi ba a kasarsu.

A cikin bidiyon, an gano karatan maza a wani wuri da yayi kama da wajen siyar da abinci suna wanke tulin kwanuka. Sun mayar da hankali sosai wajen ayyukansu yayin da suke sanye da kayan girki.

Kara karanta wannan

Rudani: Bidiyo ya nuna yadda jami'an tsaro ke dukan 'yan mata marayu a Saudiyya, an fara bincike

Wanke-wanke
Zaman Dubai Sai An Shirya: Bidiyon Wasu Karatan Maza Suna Aikin Wanke-Wanke Don Samun Na Kashewa
Asali: UGC

Maza masu kwazo a Dubai

Wasun sun suna ta dan hira yayin da suke aikatau. Gaba daya kewaye suke da kwanuka masu datti wadanda ke jiran wanki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muryoyin da ke tashi a bidiyon ya yi kama da yaruka daban-daban wanda ke nuna cewa ma’aikatan sun fito ne daga kasashe daban-daban a fadin duniya domin neman na kai a Dubai.

Kalli bidiyon a kasa:

A daidai lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya tattara martani fiye da 700 tare da ‘likes’ fiye da 10,000.

dramalady01 ta ce:

“Idan nayi aiki a nan….kwanuka da yawa za su fashe. Na rantse.

Its_Esther ta ce:

“Wannan horo ne. Hakan ba daidai bane.”

Savannah cat lover ta yi martani:

“Suna samun kudi fiye da abun da za a biyasu a Ghana kan irin wannan aikin.”

Prossie Nakanjako ta ce:

Kara karanta wannan

Ku Kama Mazajenku Da Kyau, Maza Tsada Suke A UK: Budurwa Da Ke Turai Ta Shawarci Yan Matan Najeriya

“Irin wannan aikin nake nema don na manta da tsohon saurayina. Zai hanani tunani tsawon lokaci.”

Makaryaci Ne, Ba Shinkafa Yake Siyarwa Ba: Budurwa Ta Fallasa Matashi Mai Garkuwa Da Mutane

A wani labarin, wata mai amfani da Twitter, Ayyamuus, ta bayyana yadda yan sanda suka kama wani abokinta kan zargin shiga harkar garkuwa da mutane.

A cewarta, matashin ya yi masu karyar cewa yana sana’ar siyar da shinkafa ne amma sai daga baya suka gano cewa duk karya ne.

Ya siya motoci da wani sabon gida kuma sun je har gidan don taya shi murnar bude gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel