2023: Ku Tashi Ku 'Ƙwace' Mulki Daga Hannun Dattijai, Gwamna Ya Zaburar Da Matasan Nigeria
- Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya shawarci matasan Nigeria su hada kansu domin ganin sun karbi mulki daga hannun dattijai a 2023
- Gwamnan na Jihar Kogi ya ce matasan Nigeria sun yi sake sun bar wa dattijai kujerar shugabancin kasar
- Bello ya shawarci matasan su zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya gabanin babban zaben na 2023 domin cimma burin karbe mulki a ƙasar
Ijebu-Ode, Jihar Ogun - Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi ya ce matasan Nigeria ba su nuna wa dattijai cewa 'lallai da gaske suke son karɓe shugabancin kasa ba', rahoton The Cable.
Bello, wanda tuni ya bayyana niyyarsa na yin takarar shugabancin kasa, a ranar Talata ya yi kira ga matasa su yi aiki don ganin sun 'ƙarbe' mulki daga hannun dattawa gabanin zaben 2023.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a Ijebu-Ode, jihar Ogun, a wurin wani taro da aka yi wa laƙabin: "Matasa ke da iko a hannun su'.
Wata kungiya mai suna Afenifere for Collective Transformation Act (ACT) ta shirya taron kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Da ya ke magana ta bakin Folashade Ayoade, Sakataren gwamnatin jihar Kogi, Bello ya bukaci matasa su sake shiri su hada kai gabannin zaben na 2023.
Ya shawarci matasa su dena nuna halin ko in kula game da batutuwan da suka shafi shugabanci a kasar.
Ya ce:
"Tsawon lokaci matasan Nigeria ba su nuna damuwa sosai ba kan karɓe mulki daga hannun dattawa da suka mayar da mukamin tamkar gadonsu.
"Dattijan mu suna cigaba da kwantar da hankulansu yayin zaben shugabancin kasa domin bisa alamu matasa sun bar musu matsayin."
Tolu Ajayi, direkta-janar na ACT, a jawabinsa, ya bayyana Bello a matsayin matashin Nigeria mara nuna banbancin ƙabila wanda za a iya damƙawa amanar ƙasa.
2023: Gwamnatin Adamawa Ta Bada Shaida a Kan Zaman Atiku Ɗan Nigeria Ko Akasin Haka
Bisa ga dukkan alamu ana daf da kawo karshen dambarwar da ake yi game da cancantar Atiku Abubakar na fitowa takarar shugaban kasa a babban zaben shekarar 2023.
The News ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Adamawa, a ranar 27 ga watan Yuli, ta shaidawa kotun tarayya da ke Abuja cewa Atiku Abubakar ya cancanta tsayawa takarar kujerar shugaban kasa.
Legit.ng ta tattaro cewa attoni janar na jihar Adamawa, Afraimu Jingi, yayin gabatarwa kotu hujojinsa ya shaidawa Mai Shari'a Inyang Ekwo cewa yana son a gwamutsa shari'ar da wata kungiya ta shigar kan Atiku da wasu mutum uku.
Asali: Legit.ng