Jamhuriyar Nijar Ta Musanta Karbar Tallafin Motocin N1.14bn Daga Gwamnatin Najeriya

Jamhuriyar Nijar Ta Musanta Karbar Tallafin Motocin N1.14bn Daga Gwamnatin Najeriya

  • Gwamnatin Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da Najeriya ta musanta cewa ta karbi tallafi daga gwamnatin Najeriya
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ministar kudi, Zainab Ahmed ta tabbatar da mika gudummawar motoci masu tsada da kasar
  • ‘Yan Najeriya da dama sun bayyana kaduwarsu da wannan labari duba da irin kalubalen kudaden shiga da Najeriya ke fuskanta

Nijar - Jamhuriyar Nijar ta musanta karbar motoci guda 10 masu darajar N1.1bn da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ce ta siya ne ta ba kasar saboda dalilai na tsaro.

A cewar Ministan Tsaro na Jamhuriyar Nijar, Alkassoum Indatou, babu irin wannan gudummawar da ta shiga hannun jamhuriyar Nijar mai kama da motoci.

Kasar Nijar ta magantu kan tallafin motocin Buhari
Jamhuriyar Nijar Ta Musanta Karbar Tallafin Motocin N1.14bn Daga Gwamnatin Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Indatou ya bayyana cewa jihar Zamfara ce kadai ta kawo wa kasar agaji na motoci biyar, kamar yadda jaridar Daily Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Goro a miya: Gwamnoni sun taru a Aso Rock don tattauna batun tattalin arziki, Buhari bai halarta ba

Indatou, wanda ya yi magana a madadin shugaban Jamhuriyar Nijar wajen karyata karbar tallafin motocin da fadar shugaban Najeriya ta ce ta bayar, ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sabanin abin da ministar kudi ta Najeriya, Zainab Ahmed ta bayyana, jihar Zamfara ce kadai ta baiwa yankin Maradi tallafin motoci biyar, wadanda hudu daga cikinsu tuni aka karbe su.
"Al'ummar Zamfara da ke kan iyaka da Nijar na kira ga sojojin Nijar da ke amsa kiran gaggawa cikin minti daya fiye da na kasarsu."

Bayanin ma'aikatar Kudi akan gudummawar motoci ga Nijar

A kwanakin baya ne dai ministar kudi, Zainab Ahmed ta bayyana sayen motocin, inda ta ce ra'ayi ne na shugaba Manjo Buhari mai ritaya.

Labarin dai ya haifar da musayar yawu tsakanin 'yan Najeriya.

Sai dai, Zainab ta ce duk da cewa ‘yan Najeriya na da ‘yancin magana kan dalilin da ya sa aka ba da irin wannan gudummawar, amma Buhari ma na da nasa damar yin abin da ya so kuma ya kamata, kamar yadda Punch ta kawo.

Kara karanta wannan

Assha: Darajar Naira ta sake raguwa a kasuwar hada-hadar canjin kudade

Zai yi abin da yake so: FG ta ba dalilin da yasa Buhari zai ba jamhuriyar Nijar motocin N1.5bn

A wani labarin, gwamnatin tarayya, a ranar Laraba, ta kare kudurin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kashe Naira biliyan 1.145 ga Jamhuriyar Nijar, Daily Trust ta ruwaito.

Ministar Kudi, Kasafin da Tsare-Tsare ta Kasa Zainab Ahmed, ta yi wannan tsokaci ne a lokacin da ta ke gabatar da tambayoyi bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa ya jagoranta a fadar gwamnati da ke Abuja.

Ministar, wacce ta ce shugaban kasar na da ‘yancin yanke shawara don amfanin Najeriya, ta kara da cewa "wannan ba shi ne karon farko da kasar ke ba da irin wannan gudunmawa ga makwabtanta ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel