Darajar Naira Ya Sake Yin Kasa a Kasuwar ’Yan Hada-Hadar Canji

Darajar Naira Ya Sake Yin Kasa a Kasuwar ’Yan Hada-Hadar Canji

  • Darajar kudin Najeriya, Naira ya kara samun kaskanci a kashewar canjin kudade; bakar kasuwa
  • Makwanni kadan da suka gabata ne aka yi ta cece-kuce kan tabarbarewar dajarar kudin na Najeriya
  • Majalisar dattawa ta nemi titsiye gwamnan babban bankin Najeriya, domin jin yadda za a dawo da darajar Naira

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Darajar Naira ta sake raguwa zuwa N683 kan kowacce dala a kasuwar hada-hadar canjin kudade ta FX, wacce aka fi sani da bakar kasuwa.

Rage darajar na Naira nuna faduwar darajarta da akalla N3 ko 0.4% bisa dari daga N680 da aka yi canja ta a makon jiya.

'Yan canjin suka zanta da jaridar TheCable a ranar Talata sun ce har yanzu akwai karancin kaya a kasuwar caji.

Yadda farashin Naira ya kara durkushewa a kasuwar canji
Naira ta sake durkushewa zuwa N683 kan kowace dala a kasuwar canji | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Sun sanya farashin siyan dala akan N678, farashin saye kuma a kan N683, inda suke bin ribar N5.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Nada Dangote Wata Mukami Mai Muhammanci a Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani dan canji ya ce:

"Har yanzu akwai tsananin bukata, amma ba mu da isassun daloli."

A shekarar da ta gabata, babban bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da siyar da kudaden waje ga 'yan canji.

Godwin Emefiele, gwamnan CBN, ya ce ’yan kasuwar canji sun kaucewa manufarsu ta saukaka harkallar kudaden ciki da waje, inda suka rikide zuwa dillalan yaudara.

Daga baya babban bankin ya kaddamar da bankunan ajiya don biyan bukatun jama'ar kasa baki daya.

Musayar dala da Naira babu tabbas, inji dan canji

A yau Talata, 16 ga watan Agusta wakilin Legit.ng Hausa ya ziyarci ofishin wani dan canji, Alhaji Suleiman Abdulkadir, wanda ya zanta dashi kana ya sauya wasu kudade a hannunsa.

Ya shaida cewa, yana karbar dala a kan farashin N670, sannan yana siyarwa a kan N685.

Kara karanta wannan

An kuma: Tururuwa ta cinye takardun kudaden da aka kashe a asusun inshora na NSITF

Hakazalika, ya kuma tabbatar da cewa, akwai karancin kudaden, wannan yasa idan aka kawo dala suke haba-haban siya.

A bangare guda, wani mutumin da ya halarci hajjin bana, Abdullahi Musa Abdullahi ya bayyana wa wakilin namu cewa, ya sauya dala a kan N700 kafin tafiyarsa hajjin, amma da ya dawo da saura ya siyar da ita a kan N600 saboda bukatar kudin.

Lalacewar Naira: Majalisar dattawa ta gayyaci gwamnan CBN yayin da dala ta kai N700

A wani labarin, majalisar dattawa ta gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kan faduwar darajar Naira.

Hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Olubunmi Adetunmbi (APC, Ekiti ta Arewa) ya gabatar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A halin yanzu dai darajar Naira bai wuce tsakanin N690 zuwa N700 ba kan kowacce dala a kasuwanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel