Hajj 2022: Ma'aikatar Hajji ta sanar da korar wasu manyan jami'ai a kamfanin aikin Hajji

Hajj 2022: Ma'aikatar Hajji ta sanar da korar wasu manyan jami'ai a kamfanin aikin Hajji

  • Hukumomin Saudiyya sun dakatar da wasu jami'ai bisa zarginsu da kawo tsaiko a ayyukan Hajjin bana
  • Hukumomin sun kuma bayyana cewa, ba za su bari wani abu ya kawo cikas ga jin dadin alhazai ba
  • A ranar Alhamis ne za a fara gudanar da ayyukan aikin Hajji tare da mutane akalla miliyan daya daga sassan duniya

Riyadh, Saudiyya - Ma'aikatar aikin Hajji ta Saudiyya ta sanar da korar wani shugaba da wani babban jami'i a "daya daga cikin kamfanonin aikin Hajji" da ke gudanar da ayyukan hajjin bana.

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta ce an cire su ne saboda rashin samar da isassun kula ga alhazai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ruwaito a safiyar ranar Alhamis.

Saudiyya ta dakatar da wasu jami'ai bisa kawo cias ga alhazai
Hajj 2022: Ma'aikatar Hajji ta sanar da korar wasu manyan jami'ai a kamfanin aikin Hajji | Hoto: thenationalnews.com
Asali: UGC

Ma'aikatar ta ce matakin ya biyo bayan hada kai da kwamitin gudanarwa na kamfanin da kuma lura da ma'aikatar ta yi.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan INEC Sun Rufe Kwamishina a Ofishinsa Saboda Rashin Biyansu Hakokinsu

Sanarwar ta kuma ce an mika jami'an biyu zuwa sashen bincike, The National News ta kawo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar Alhamis ne za a fara gudanar da aikin Hajji, wanda shi ne muhimmin ginshikin addinin Musulunci, tare mahajjata miliyan daya daga sassan duniya daban-daban.

Ma’aikatar ta sake nanata cewa tana sa ido sosai kan duk wasu ayyuka da hukumomi da kamfanonin da ke aiki a lokacin aikin Hajji ke yi domin tabbatar da ingancinsu.

Ta ce tana kuma sa ido kan duk wani cin zarafi da kuma magance su nan take a wani bangare na kokarin da take na bibiyar tsaro da jin dadin mahajjata, rahoton Arab News.

Ma'aikatar ta jaddada cewa ba za ta kyale ba kuma ba za ta amince da duk wata gazawa da ta shafi hidimar alhazai ba.

Kara karanta wannan

Garin neman kiba: Banki ya fece da kudin kwastomomi garin neman rancen miliyoyi

Hajji 2022: Maniyyata 1,000 sun yi cirko-cirko a sansanin Alhazai na jihar Kano

A wani labarin, shugaban hukumar jin daɗin Alhazai na jihar Kano, Alhaji Mohammad Abba Dambatta, ya ce kamfanin jiragen sama na Azman Air ya kwashe maniyyata 1,386 zuwa ƙasa mai tsarki.

Rahoton Leadership ya tattara cewa maniyyata 1,000 na jihar Kano na nan a sansanin Alhazai suna jiran jirgin da zai zo ya kwashe su zuwa Saudiyya.

Ɗanbatta ya ce har yanzun akwai ragowar maniyyata 1,000 da ba su tashi zuwa ƙasa mai tsarki ba. Ya ƙara da cewa maniyyata 86 ba su samu Visar su ba har zuwa yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel