Rasha so take ta shafe tarihinmu a doron kasa, Shugaban Ukraine ya sake bayani

Rasha so take ta shafe tarihinmu a doron kasa, Shugaban Ukraine ya sake bayani

  • Shugaban kasar Ukraine ya sake fitowa ya yi magana kan yadda Rasha ke son ganin bayan tarihin kasar
  • Shugaba Zelelensky ya yi kira ga Yahudawa a duniya su tashi tsaye domin kare wani wurin tarihi da Rasha ta farmaka
  • Wannan batu nasa na zuwa ne sa'o'i kadan bayan da Rasha ta harba makami mai linzami kan wata husumiyar talabijin a Kyiv

Kyiv, Ukraine - Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky a ranar Laraba ya zargi kasar Rasha da ta kaddamar da farmaki kan kasarsa da neman shafe 'yan kasar Ukraine, kasarsu da kuma tarihinsu a doron kasa.

A wani jawabin da ya yi, shugaban na Ukraine ya ce harin makami mai linzami na kisan kiyashi da aka kai kan kasarsa ya nuna yadda kasar Rasha ke shirin kassara birnin Kyiv, NDTV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yakin Rasha da Ukraine: Abubuwa 12 da suka faru bayan tattaunawar sulhun Rasha da Ukraine

Shugaba Zelensky na Ukraine ya yi magana kan harin Rasha
Rasha so take ta shafe tarhinmu a doron kasa: Shugaban Ukraine ya sake bayani | Hoto: sawahpress.com
Asali: UGC

Harin da aka kai a daren ranar Talata ya lalata babban husumiyar talabijin na Kyiv, wanda aka gina a Babi Yar, wurin da aka yi kisan gillar Yahudawan Kyiv a yakin duniya na biyu.

Hukumomin Ukraine sun ce mutane biyar ne suka mutu a harin, a bangaren Zelensky kuma, ya ce hari kan wurin ya jaddada barazanar Rasha ga shafe asalin Ukraine da abubuwan tarihinta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalaman Zelensky game da harin da Shugaba Vladimir Putin ya yi kan Ukraine:

"Ba su san komai ba game da babban birninmu ba, game da tarihinmu ba. Kawai dai an basu odar shafe tarihinmu ne, su shafe kasarmu. Su shafe mu baki daya."

Shugaban na Ukraine ya koka da cewa a karkashin mulkin Tarayyar Sabiyet, hukumomi sun gina hasumiyar ta talabijin da wani katafaren filin wasanni a yanki na musamman na Turai, wanda ya kasance wurin ibada, kana wurin mai dimbin tarihi.

Kara karanta wannan

Ku zo ku taya mu yaki: Shugaban Ukraine na neman sojoji daga Najeriya da sauran kasashe

Ya kamata Yahudawa su farga

Hakazalika, a bayanansa ya kuma bukaci Yahudawa a duk fadin duniya su yi magana kan wannan wuri mai dimbin tarihi da ake son lalatawa, kamar yadda Channels Tv ta tattaro.

Ya kara da cewa:

“A yanzu da Yahudawan duniya nake magana. Ba ku ga abin da ke faruwa ba? Shi ya sa yake da matukar muhimmanci cewa miliyoyin Yahudawa a fadin duniya kada su yi shiru a halin da ake ciki.”

Hakazalika, ya bayyana cewa, a hankali ana kara tada akidar kin jinin Yahudawa a duniya, kamar yadda a baya aka samu lokacin yakin duniya na biyu.

Yakin Rasha da Ukraine: Abubuwa 12 da suka faru bayan tattaunawar sulhun Rasha da Ukraine

A wani labarin, wakilan Rasha da Ukraine a ranar Litinin 28 ga watan Fabrairu sun fara tattaunawar zaman lafiya tun bayan da shugaba Vladimir Putin ya umarci dakarunsa su mamaye Ukraine a makon jiya.

Kara karanta wannan

An shiga tsakani: Za a yi tattaunawar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha yau Litinin

Wakilan kasashen biyu sun gana a kan iyakar Belarus da Ukraine don tattaunawa ta farko. An tattaro cewa babban makasudin taron shine tattauna batun tsagaita wuta da kuma kawo karshen yaki akan Ukraine.

Legit.ng ta tattaro muku abubuwan da suka faru bayan tattaunawar zaman lafiya tsakanin kasahen biyu kamar yadda The Asean Post ta ruwaito:

Asali: Legit.ng

Online view pixel