Tirkashi: Uwa ta kashe 'ya'yanta biyar saboda kishi, ta hadu da fushin alkali

Tirkashi: Uwa ta kashe 'ya'yanta biyar saboda kishi, ta hadu da fushin alkali

  • Wata uwa mai shekaru 28 ta gamu da fushin alkali bayan ta kashe 'ya'yanta har su biyar
  • An tattaro cewa kishin ganin hoton mijinta tare da sabuwar abokiyar zamansa ce ya tunzurata har ta kai ga aikata hakan
  • Yaran da ta kashe suna tsakanin shekaru daya zuwa takwas ne, inda babban cikinsu kuma cikon na shida ya tsira da ransa

Kasar Jamus - Wata kotu ta yanke wa wata mata a birnin Solingen na yammacin Jamus hukuncin daurin shekaru 15 bayan sanmunta da laifin kashe biyar daga cikin yaranta guda shida.

Yaran da ta halaka suna a matsakin shekara daya zuwa takwas, jaridar Vanguard ta rahoto.

Tirkashi: Uwa ta kashe 'ya'yanta biyar, ta hadu da fushin alkali
Tirkashi: Uwa ta kashe 'ya'yanta biyar, ta hadu da fushin alkali Hoto: Thisday
Asali: UGC

Kotun wacce ke da zama a birnin Wuppertal ta kasa gano wani dalili da zai sa a yi wa matar mai shekaru 28 a duniya uzuri, saboda haka ta soke batun sakinta bayan kammala wa'adin shekaru 15 a gidan yari.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da mijin da ya soka wa matarsa almakashi, ta sheka lahira

Babban dan matar ya tsallake tuggun nata.

A yayin shari'ar, mai shigar da karar ya yi zargin cewa ta fara gusarwa da yaran hankali ne sannan sai ta jefa su ruwa ko ta shake su daya bayan daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'an da ke binciken lamarin sun yarda cewa ganin hoton mijinta da sabuwar matarsa shine ya karfafa mata gwiwar aikata ta'asar, wanda ya gigita kasar Jamus.

Bayan nan ta aika masa da sakon cewa ba zai sake ganin yaran ba. An gano gawarwakin yaran a gadajensu a ranar 3 ga watan Disamban 2020, rahoton Independent.

Matar ta dage cewa wani ne ya shigo gidanta, ya daure ta sannan ya tursasa ta aika sakon kafin ya kashe yaran.

Kwararrun likitocin mahaukata ba su sami wata shaida ta mummunar tabin hankali tare da ita ba.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sintiri sun yi ram da mutumin da ke bayyana wa mata al'aurarsa

Lauyan da ke kare ta ya nemi a sake ta bisa hujjar cewa akwai kokwanto kan ko wacce yake karewa ce ta aikata kisan.

Kotun ta gano cewa mahaifiyar yaran wacce ta sha jefa kanta a gaban jirgin kasa da ke tafiya a tashar Dusseldorf ce ta kashe su.

Yaran sune; Melina, 1, Leonie, 2, Sophie, 3, Timo, 6, da Luca, 8. Ta tura babban danta wanda ya tsira zuwa wajen kakarsa.

Ku taimaka ku kaini kurkuku, ba zan iya zama da matata ba - Matashi ya koka

A wani labarin, wani magidanci mai shekaru 30 a duniya wanda ya ce ya gaji da rigimar matarsa ya roki yan sanda da su tsare shi.

A cewar mutumin sam ba zai iya ci gaba da kasancewa tare da matar tasa ba, inda ya ce gara masa zaman gidan kurkuku, rahoton Pulse Nigeria.

Ya ce: “Ina son tafiya gidan kurkuku, ba zan iya ci gaba da jure halin matata ba.”

Kara karanta wannan

'Yan dadi Afrika: Yadda mata 3 suka bar kasashensu na turai suka kauro Afrika, Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel