'Yan sanda sun yi ram da mijin da ya soka wa matarsa almakashi, ta sheka lahira

'Yan sanda sun yi ram da mijin da ya soka wa matarsa almakashi, ta sheka lahira

  • Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta yi caraf da magidanci da ya soka wa matarsa almakashi ta mutu
  • Makwabta sun dinga jin ihun matar wacce mijin ya kulle a daki ya na duka, sai dai ya ki budewa duk da rokon da ake masa
  • 'Yan sanda da kansu suka balle kofar inda suka tarar da ita kwance cikin jini, kafin a mika ta asibiti kuma likita ya tabbatar da mutuwarta

Ogun - Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta cafke wani magidanci mai shekaru 24 a duniya mai suna Mojiyagbe Olamilekan, kan zarginsa da burma wa matarsa mai suna Seun Alkamashi a ciki.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ta sanar da manema labarai a garin Abeokuta, babban birnin jihar, cewa wanda ake zargin mazaunin yankin Oke Ola ne da ke Ode Remo a karamar hukumar Remo ta arewa ta jihar.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sintiri sun yi ram da mutumin da ke bayyana wa mata al'aurarsa

Daily Trust ta ruwaito cewa, Seun ta sheka lahira kuma an cafke mijin ta a ranar Laraba da ta gabata.

'Yan sanda sun yi ram da mijin da ya soka wa matarsa almakashi, ta sheka lahira
'Yan sanda sun yi ram da mijin da ya soka wa matarsa almakashi, ta sheka lahira. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce kamen ya biyo bayan wani kiran da 'yan sanda suka samu na gaggawa kan cewa wanda ake zargin ya rufe kansa da matarsa a daki inda ya dinga dukan ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ihun matar ne ya janyo hankalin makwabtan su ,wadanda suka dinga kokarin sa wanda ake zargin ya bude kofar amma ya ki, Daily Trust ta wallafa.

"Bayan samun kiran gaggawan DPO na yankin Remo, CSP Olayemi Fagbohun ya aike jami'ansa kuma sun gaggauta zuwa wurin inda suka balle kofar dakin ma'auratan.
"An tarar da marigayiyar kwance cikin jini kuma an gaggauta mika ta asibitin jihar da ke Isara Remo inda likita ya tabbatar da mutuwar ta.

Kara karanta wannan

Matsolo ne, baya bani kuɗi: An kama matar aure da ta haɗa baki da gardawa 3 don garkuwa da mijinta

“A take aka kama mijin tare da kulle shi yayin da aka adana gawarta a ma'adanar gawawwaki da ke asibitin domin bincikar abinda ya kashe ta," kakakin rundunar 'yan sandan yace..

Ya ce bisa umarnin kwamishinan 'yan sandan jihar, Lanre Bankole, an mayar da wanda ake zargin sashin binciken masu kisan kai na jihar kuma za a mika shi gaban kotu bayan kammala bincike.

An tsinci gawar jami'in kwastam da miyagu suka yi garkuwa da shi

A wani labari na daban, an tsinci gawar jami'in hukumar kwastam da ake sace a jihar Ogun a ranar Talata da ta gabata, Daily Trust ta wallafa.

Wasu miyagu da ake zargin 'yan sumogal ne suka yi wa jami'an kwanton bauna yayin da suka fita sintiri a karamar hukumar Yewa ta kudu da ke jihar kuma suka sace jami'ai biyu.

An tsinta gawar daya daga cikin jami'an a wani rafi kusa da kauyen Fagbohun da ke karamar hukumar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel