Ku taimaka ku kaini kurkuku, ba zan iya zama da matata ba - Matashi ya koka

Ku taimaka ku kaini kurkuku, ba zan iya zama da matata ba - Matashi ya koka

  • Rayuwar aure ta yi wa wani magidanci zafi inda ya gwammaci zama a kurkuku fiye da gidansa
  • Magidancin ya roki yan sanda a kan su jefa shi kurkuku maimakon zama gida daya da matarsa
  • Ya ce matarsa fitinanniya ce ta bugawa a jarida domin kullun sai sun yi fada

Wani magidanci mai shekaru 30 a duniya wanda ya ce ya gaji da rigimar matarsa ya roki yan sanda da su tsare shi.

A cewar mutumin sam ba zai iya ci gaba da kasancewa tare da matar tasa ba, inda ya ce gara masa zaman gidan kurkuku, rahoton Pulse Nigeria.

Ku taimaka ku kaini kurkuku, ba zan iya zama da matata ba - Matashi ya koka
Ku taimaka ku kaini kurkuku, ba zan iya zama da matata ba - Matashi ya koka Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Ya ce:

“Ina son tafiya gidan kurkuku, ba zan iya ci gaba da jure halin matata ba.”

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da mijin da ya soka wa matarsa almakashi, ta sheka lahira

Mutumin dan kasar Albaniya wanda ya fito daga Guidonia, wani gari a wajen birnin Rome ya shafe tsawon watanni da dama tsare a gida kan laifin da ke da nasaba da miyagun kwayoyi.

Kuma ya rage masa shekaru da dama kafin ya kammala hukuncin daurin da aka masa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ta rahoto.

A ranar 23 ga watan Oktoba, ya je barikin yan sanda na Tanenza Carabinieri da ke garin Guidonia domin rokonsu a kan su jefa shi kurkuku saboda ba zai iya ci gaba da hukuncin daurin da aka yi masa a gida daya da matarsa ba.

Matashin ya fada ma yan sanda cewa:

“Ku kama ni, ba zan iya jure zama gida daya da matata ba kuma, na gwammaci zaman kurkuku.”

A cewarsa, matarsa tana da fitina sosai ta yadda kullun sai sun yi fada, lamarin da yasa ya gwammaci zaman kurkuku fiye da gidansa.

Kara karanta wannan

Bayan lashe zabe, sabon shugaban matasan PDP ya magantu kan manufarsa akan APC

An nakalto Kyaftin Francesco Giacomo Ferrantte na Tivoli Carabinieri yana cewa:

“Yana zama a gida tare da matarsa da iyalinsa. Abubuwa sun daina tafiya daidai. Ya ce, saurara, rayuwar gidana ya zama tamkar a wuta, ba zan iya ba, Ina son tafiya kurkuku.”

Bayan rokon da magidancin yayi, sai Carabinieri ya sanar da hukumar shari’a sannan aka mayar da shi gidan yari kan karya dokar tsare sa da aka yi a gida.

Matar da ta siya wa mijinta mota ta ce za ta iya siya masa jirgin sama idan tana da hali

A wani labarin, wata ‘yar Najeriya Gbadewole Olubunmi Mary da ta bai wa mijinta kyautar sabuwar mota kirar Mercedes Benz a ranar zagayowar ranar aurensu na 7, ta ce za ta so yi masa kyautar jirgin sama idan Allah ya albarkace ta.

Da take magana da @bbcnewsyoruba, matar ta ce ta saya wa mijinta motar ne saboda shi mutum ne mai kyauta.

Kara karanta wannan

Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami

A cewar Mary, mutane ba sa ba mijinta kyaututtuka duk da cewa shi mutum ne mai bayarwa. Ta ce tana ta tunanin baiwa mutumin wani babban kyauta tun lokacin da suka haifi dan su na farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel