An fitar da jerin Musulmi 500 mafi ƙarfin faɗa aji a duniya, Buhari, Ɗangote, Ɗahiru Bauchi da Zakzaky na ciki

An fitar da jerin Musulmi 500 mafi ƙarfin faɗa aji a duniya, Buhari, Ɗangote, Ɗahiru Bauchi da Zakzaky na ciki

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari yana cikin jerin musulmin duniya 500 mafi karfin fada aji kamar yadda cibiyar nazarin addinin Islama da ke Amman a Jordan ta fitar.

A kowane shekara cibiyar tana fitar da sabbin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya.

Shugaba Buhari ne mutum na 16 a cikin jerin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya a bana kamar yadda The Muslim 500 ta fitar.

Jerin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya, Buhari da Dahiru Bauchi da Dangote na ciki
Musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya, Buhari da Dahiru Bauchi da Dangote na ciki. Hoto: The Muslim 500
Asali: Facebook

Sauran 'yan Najeriya da ke cikin jerin sunayen sun hada da Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Sheikh Ibrahim Saleh.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Shugaban NHRC da sauran manyan lauyoyi 71 da suka samu girmamawa ta SAN

Alhaji Aliko Dangote, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Yakubu Musa Katsina, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky suma suna ciki.

Jerin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya, Buhari da Dahiru Bauchi da Dangote na ciki
Shugaba Muhammadu Buhari ne na 16 cikin jerin musulmi 500 masu fada aji. Hoto: The Muslim 500
Asali: Facebook

Jerin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya, Buhari da Dahiru Bauchi da Dangote na ciki
Musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya, Buhari da Dahiru Bauchi da Dangote na ciki. The Muslim 500
Asali: Facebook

A cewar cibiyar:

"Duk wani da ke da karfin fada aji ko ta gargajiya, akida, kudi, siyasa ko waninsa kuma zai iya kawo canji a duniyan musulmi yana iya fadowa cikin jerin.
"Fitar da sunayensu baya nufin muna goyon bayan ra'ayoyinsu ko akidunsu, kawai dai abin da ake duba wa shine karfin fada aji da suke da shi."

Mutane mafi karfin fada aji a duniyar musulmi

A cewar Muslim 500, Dan kwallon Liverpool, Mohammed Salah, Sadio Mane, Paul Pogba, Zinedine Zidane suma suna cikin jerin masu karfin fada aji.

Amma wadanda ke kan gaba a jerin sun hada da

  • Shugaba Recep Tayyip Erdoğan, Shugaban kasar Turkiyya
  • Sarki Salman bin Abdul-Aziz Al-Saud na kasar Saudiyya
  • Ayatollah Hajj Sayyid Ali Khamenei, shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran
  • Sarki Abdullah II Ibn Al-Hussein na kasar Jordan
  • Mai shari'a Sheikh Muhammad Taqi Usmani, malami kuma shugaban Deobandi
  • Sarki Mohammed VI, Sarkin kasar Morocco
  • Mai martaba, Janar Sheikh Mohammed bin Zayed Al-Nahyan, yarima mai jiran gado na Abu Dhabi kuma mataimakin babban kwamandan sojojin UAE
  • Ayatollah Sayyid Ali Hussein Sistani, Marja na Hawza, Najaf da Iraq
  • Sheikh Al-Habib Umar bin Hafiz, Shugaban Dar Al Mustafa, Tarim, Yemen
  • Sheikh Salman Al-Ouda, Mai wa'azi kuma makaranci

Kara karanta wannan

Wakilin Birtaniya ya dira kotu domin shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB

Ga dai cikaken jerin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji na 2022 a shafin Muslim 500.

Asali: Legit.ng

Online view pixel