Jerin Sunaye: Shugaban NHRC da sauran lauyoyi 71 da suka samu girmamawa ta SAN

Jerin Sunaye: Shugaban NHRC da sauran lauyoyi 71 da suka samu girmamawa ta SAN

Anthony Ojukwu, babban sakatare hukumar kare hakkin bil-adama na kasa, NHRC, ya zama babban lauyan Nigeria mai mukamin SAN.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Ojukwu na daya daga cikin lauyoyi 72 da kwamitin alfarma ta lauyoyi, LPPC, ta karrama da mukami SAN a taronta na 149 a ranar Alhamis.

Lauyoyi 130 ne aka tattara sunayensu don tantance wadanda za a yi wa karin girman na SAN tun a watan Satumba.

Jerin Sunaye: Shugaban NHRC da sauran lauyoyi 71 da suka samu girmamawa ta SAN
Anthony Ojukwu, Shugaban NHRC ya samu mukamin SAN. Hoto: The Cable
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga cikinsu 95 masu aikin lauya ne a kotuna sannan 35 kuma masu koyarwa ne a makarantu. Mutane 72 ne suka yi nasara yayin da 58 ba su samu mukamin ba.

Daga cikin fitattun mutane da suka samu mukamin na SAN akwai Ikeazor Akaraiwe, tsohon mataimakin shugaban kungiyar lauyoyi na kasa, NBA da Emeka Obegolu, sakataren NBA.

Read also

An daure dalibai 19 da aka kama sun shiga kungiyar asiri a Jami’a bayan doguwar shari'a

LPPC cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce za a yi bikin rantsar da SAN din 72 a ranar 8 ga watan Disamban 2021 karkashin jagorancin alkalin alkalai na kasa a kotun koli da ke Abuja, Channels TV ta ruwaito.

Har wa yau, LPPC ta kuma tunatar da al'umma cewa ta kafa wata kwamiti don bita kan ka'idojin bada mukamin na SAN daga shekarar 2023.

Ga jerin sunayen sabbin wadanda aka nada SAN:

 1. Adeniyi Anthony Ademuyiwa
 2. Umeh Philip Ndubuisi Evaristus
 3. Ovrawah Ogaga
 4. Afuba Peter Aguigom
 5. Ajose-Adeogun Olaotan Olusegun
 6. West-Idahosa Ehiogie
 7. Awa Uche Sunday
 8. Mekwunye Charles Dumbiri
 9. Oladoja Tajudeen Olaseni
 10. Akaraiwe Ikeazor Ajovi
 11. Omotosho Francis
 12. Onuzulike Felix Anayo
 13. Oru Marcelluous Eguvwe
 14. Ihua-Maduenyi Charles Udoka
 15. Agbola Adeleke Olaniyi
 16. Uzuegbu Benjamin Chukwudi
 17. Akinola James Akingbola
 18. Ihediwa Uchenna Chinyere
 19. Adeluola Olukayode Oluwole
 20. Olotu Bolarinwa
 21. Hassan Usman El-Yakub
 22. Olorunfemi Ayo Abraham
 23. Atabo Reuben Okpanachi
 24. Fapohunda Adekola Olawale
 25. Okoli Ikenna
 26. Mordi Mark Okeibunor
 27. Seriki Sheriff Rotimi
 28. Opara Victor Ugwuezumba
 29. Ndayako Mohammed
 30. Ojo Adekunle Akanbi
 31. Adele John Ogwu
 32. Wodu Kemasuode
 33. Ayinla Salman Jawondo
 34. Obiora Edwin Sunday Chukwujekwu
 35. Abdulhamid Mohammed
 36. Atung Samuel
 37. Itula Fredricks Ebos
 38. Anuga George Audu
 39. Mustapha Dauda Adekola
 40. Idris Ibrahim Agbomere
 41. Gbadamosi Kazeem Adekunle
 42. Aliyu Kabir
 43. Nworka Chidi Benjamin
 44. Abdul-Rasheed Muritala Oladimeji
 45. Kotoye Adeyinka Moyosore
 46. Obegolu Emeka Jude-Phillipe
 47. Aruwa Shaibu Enejoh
 48. Somiari Sammie Abiye
 49. Onwuenwunor Clement
 50. Omotunde Adeola Rasaq
 51. Mogboh Anthony Obinna
 52. Emeka Chijuoke Ogugua Precious
 53. Lough Simon Asamber
 54. Adedipe Ayodeji
 55. Kuti Afolabi Fatai
 56. Fatogun Eyitayo Ayokunle
 57. Eko Ejembi Eko
 58. Usman Jacob Johnson
 59. Sani Abdulaziz Mohammed
 60. Burkaa Matthew Gwar
 61. Hussaini Ishaq Magaji
 62. Ogungbade Oluwasina Olarenwaju

Read also

Muna farin cikin soke dokokin COVID-19 a Masallacin Makkah da Madina: Hukumar jin dadin Alhazai

Masu karantarwa

 1. Oyewo Ajagbe Toriola
 2. Omorogbe Oluyinka Osayame
 3. Ojukwu Anthony Okechukwu
 4. Ijaodola Rasheed Jimoh
 5. Sodipo Bankole Adekunle
 6. Wigwe Christian Chizindu
 7. Agbonika Josephine Aladi Achor
 8. Sanni Abiola Olaitan
 9. Omoregie Edoba Bright
 10. Abdullahi Ibrahim

Source: Legit.ng

Online view pixel