Abba Gida Gida da ‘Yan takara 3 da Aka Gwabza da Su Kafin Lashe Zaben Gwamna

Abba Gida Gida da ‘Yan takara 3 da Aka Gwabza da Su Kafin Lashe Zaben Gwamna

  • Hukumar INEC ta kasa ta shirya zaben Gwamnoni a wasu Jihohi 28 a shekarar nan
  • Akwai inda aka yi gumurzu kafin a samu jam'iyyar hamayya ta yi nasara a takarara
  • Jam'iyyar NNPP ta fafata da APC a Kano, haka lamarin yake da PDP a Bauchi da Zamfara

Abin da rahoton nan ya yi shi ne tattaro jihohin da ‘yan takara ko kuma Gwamnoni masu-ci da suka kai ruwa-rana kafin samun nasara a 2023.

Cikin Gwamnonin da su ka yi galaba a saukake akwai; Mai Mala Muni (Yobe), Babajide Sanwo-Olu (Legas), AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara)

Haka zalika Babagana Zulum (Borno) ya lashe zaben tazarce ba tare da wani gumi a APC ba.

A gefe guda, Gwamnoni kamar Dapo Abiodun (Ogun) da Abdullahi Sule (Nasarawa) sun fuskanci barazana a zabe, dukkansu daga jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Bayan Korar Shugaban PDP, Wike Ya Fallasa Facakar Biliyoyin da Aka Yi a 'Yan Watanni

Irinsu Uba Sani (Kaduna), Ahmed Aliyu (Sokoto), da Kefas Agbu (Taraba) sun samu nasara a kan PDP da NNPP, amma abin bai zo masu da sauki ba.

A Neja, Jigawa, Katsina da Benuwai, APC ta ci zabe cikin sauki. Haka abin yake ga jam’iyyar adawa ta PDP a jihohin Oyo da Ribas a yankin Kudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abba Gida Gida
Abba Gida Gida a Kano Hoto: @Ibraheemz01
Asali: Facebook

Jihohi da aka yi gumurzu

1. Zamfara

Dr. Dauda Lawal Dare ya doke Gwamna Bello Matawalle a Zamfara duk da irin karfin da jam’iyyar APC tayi da tarihin rashin nasarar PDP tun daga 1999.

A zaben Gwamnan, Dare da jam’iyyar PDP sun yi galaba a kan tsoafaffin Gwamnoni; Abdulaziz Yari, Mahmud Shinkafi da kuma Ahmad Yariman Bakura.

Jiga-jigan da APC ta dogara da su a Zamfara sun hada da Kabiru Marafa, Sahabi Yau, Ibrahim Wakala, Aminu Jaji, Hasan Nasiha, amma PDP ta lashe zabe.

Kara karanta wannan

Jerin Duka Shugabannin PDP 9 da Aka Yi Rabuwar Tsiya da Su Daga 1999 zuwa 2023

2. Kano

Abba Kabir Yusuf ya yi nasara a kan jam’iyyar APC mai-ci a jihar Kano, wannan karo ya doke Nasiru Yusuf Gawuna da ‘yan takaran PDP, ADC, ADP da PRP.

APC ta na da ‘yan majalisun tarayya da manyan ‘yan siyasa irinsu Kabiru Gaya, Rabiu Bichi, Murtala Garo, Abdullahi Abbas, amma su ka ji kunya a 2023.

Sauran jagororin adawa a Kano da NNPP ta samu sa’a a kan sun hada da Sadiq Wali, Bala Gwagwarwa, Yunusa Dangwani, Amiu Wali da Bello H. Gwarzo.

3. Bauchi

A jihar Bauchi, Bala Mohammed ya zarce a mulki ta hanyar doke AVM Abubakar Siddique da tulin jagororin APC da suka dage wajen ganin an kifar da PDP.

Baya ga ‘yan siyasa, dattawan jihar Bauchi irinsu Bello Kirfi sun rantse sai Bala Mohammed ya fadi zabe, a karshe Gwamnan ya ba APC tazarar kuri’u 93, 000.

Kauran Bauchi ya yaki tsofaffin gwamnoni kamar Adamu Mu’azu, M. A. Abubakar, Isa Yuguda da Ministoci da kusoshi, har da ‘yan PDP irinsu Yakubu Dogara.

Kara karanta wannan

"An Hada-Kai da INEC, Za a Murde Zaben Gwamna a Jihar Adamawa" Inji Jam’iyyar PDP

Gwamnan Kano ya soki mai jiran gado

A rahoton da mu ka fitar a baya, an ji Abdullahi Umar Ganduje ya ce shawarwarin da Injiniya Abba Kabir Yusuf yake badawa tun yanzu ba su da gindin zama.

Abba Gida Gida wanda shi ne Gwamna mai jiran gado a Kano ya ce ba zai daina bada shawarwari ba duk da gwamnati mai-ci ta na ganin shisshigi ne yake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel