Bikin yancin kai: ‘Yan Najeriya sun yi martani yayin da Shugaba Buhari ya yi kira ga hadin kai

Bikin yancin kai: ‘Yan Najeriya sun yi martani yayin da Shugaba Buhari ya yi kira ga hadin kai

  • Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu yayin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga hadin kan kasar
  • Da dama sun zargi Shugaban kasar a kan yanayin rashin hadin kai da kasar ta tsinci kanta a ciki wanda ya kai ga har wasu na neman ballewa
  • Wasu kuma sun yaba masa tare da jinjina kan yadda shi da sojojin kasar suka sadaukar da ransu don ganin abubuwa sun daidaita

Abuja - Biyo bayan kiran da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na hadin kan kasar, yan Najeriya da dama sun shiga shafukan sada zumunta don maida martani akan kalamansa.

Yayin da mutane da yawa suka zarge shi kan yanayin da haɗin kan ƙasar ke ciki a halin yanzu wanda yake a mafi ƙanƙantarsa, wasu kuma sun yaba masa da yin aiki mai kyau don haɗa kan ƙasa.

Read also

Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a

Bikin yancin kai: ‘Yan Najeriya sun yi martani yayin da Shugaba Buhari ya yi kira ga hadin kai
Bikin yancin kai: ‘Yan Najeriya sun yi martani yayin da Shugaba Buhari ya yi kira ga hadin kai Hoto: www.icirnigeria.org
Source: UGC

Ku tuna cewa wasu mutanen kudu maso gabas da kudu maso yamma suna ta kira ga neman ballewa kan abin da suka bayyana a matsayin rashin adalci daga arewa da kuma mummunan yanayin tattalin arzikin da ke fuskantar al’umma.

Ga wasu martani bayan Shugaba Buhari yayi kira ga hadin kai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mathew Obisesan

"Yanayi mafi muni a rayuwar kasarmu shine zamanin gwamnatin da Buhari ke jagoranta. Duk wanda ya tsira daga wannan gwamnatin ya cancanci lambar yabo ta tserewa daga kangin bauta, talauci, kashe-kashe marasa iyaka da wahalar tattalin arziki.
"A ganina, muna murnar gazawa ne kawai a shekaru 61 da muka yi a matsayin kasa. Ba za a iya samun 'yancin kai ba tare da 'yancin faɗin albarkacin baki, adalci, daidaito, kare rayuka da dukiyoyin jama'a ba a matsayin babban jigon kwangilar zamantakewa da ci gaba mai ɗorewa."

Read also

Hoton tsohon rasit da ke nuna an siya buhu 40 na siminti kan N1520 ya janyo cece-kuce

Odey Neo

"A koyaushe za mu tuna da kai a matsayin mutumin da ya taɓa mulkin Najeriya kuma ya lalata ci gaban tattalin arziƙi da ci gaba a Najeriya da kashe duban 'yan ƙasa marasa laifi ina fatan shaidan ya yiwa gidanka kebewa na musamman don azabtar da kai."

Adamu Muhammad

"PMB da manyan sojojin Najeriya da yawa sun sadaukar da rayuwarsu don Najeriya ɗaya, kuma sun yi nasara, mu sauran yan Najeriya za mu kare nasararsu, kuma za mu yi nasara kan sharrin masu raba kawunan."

Osita Ezebuike

"Najeriya ba ta aiki. Kuma PMB bai zo don yin aiki ba. Tunawa da ranar yanci abin haushi ne."

Dan majalisar tarayya ke daukar nauyin Sunday Igboho da Nnamdi Kanu, Buhari ya yi ikirari

A baya mun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ikirarin cewa wani dan majalisar tarayya ne ke da alhakin daukar nauyin masu kira-kirayen neman ballewar kasar nan.

Read also

Boko Haram sun gurgunta mulki a Neja, sun kayyade shekarun aurar da 'ya'ya mata

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga kasar a matsayin wani bangare na bikin ranar 'yancin kai.

Ya bayyana cewa an gano hakan ne yayin da ake gudanar da bincike bayan kamun Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar neman kasar Biyafara da kuma Sunday Igboho, shugaban masu fafutukar kasar Yarbawa.

Source: Legit.ng

Online view pixel