Hoton tsohon rasit da ke nuna an siya buhu 40 na siminti kan N1520 ya janyo cece-kuce
- 'Yan Najeriya sun yi tururuwar martani kan wani rasit na 1989 wanda ya bayyana an siyasa buhun siminti a arha
- A wata wallafar da ta bazu a Instagram, Tunde Ednut wanda ya wallafa takardar ya tambaya nawa ne kudin kayan gini yanzu
- A yayin da wasu jama'a suka ce ya fi sauki a gina gida a shekarun baya, wasu sun ce ba haka ba ne saboda lokacin babu kudin
Wani rasit da Tunde Ednut ya wallafa a Instagram yadda aka siya buhu 40 na siminti wanda aka siya kan kudi N1520.
Hotunan takardun shaidar siyan simintin an ga sunan wani Moshood Ajayi a kai wanda ya siya a watan Mayun 1989.
Shin da gaske rayuwa ta fi sauki a baya?
A sani cewa, Legit.ng da kan ta ba ta tantance hoton rasit din ba ko kuma samun karin bayani yayin rubuta wannan rahoton.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tuni hoton ya janyo maganganu daban-daban daga 'yan Najeriya inda suka dinga nuna mamakinsu kan yadda sauyi ya zo kasar nan da wuri.
Tuni rasit din ya samu martani daruruwa daga 'yan Najeriya wadanda suka dinga tafka muhawara kan abinda ya faru da kasar nan.
Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin martanin kamar haka:
vstarma ya ce: "Wannan Dangote bai yi wa jama'a abun kirki ba."
jiggy_teeens cike da nishadi ta ce: "Tabdijan, ashe na cinye kudin katon gida jiya?"
kaftanmogul_ ya ce: "Abubuwa sun kasance masu sauki ga iyayenmu ba kamar yanzu ba. Wannan zamanin muna ganin abubuwa."
wendy_fierce yace: "A lokacin da rayuwa ta ke da sauki kadan."
officialaisha05 cewa ta yi: "Tabbas, amma wasu mutanen ba su iya siyan shi a wancan lokacin."
DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016
A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta karrama Muhammad Abu Ali, soja mai mukamin laftanal kanal kuma kwamandan bataliya ta 272 a baya wanda Boko Haram suka kashe a 2016.
TheCable ta ruwaito cewa, a ranar 4 ga watan Nuwamban 2016, 'yan ta'addan Boko Haram sun halaka Ali yayin da suka kai wa bataliya ta 119 farmaki da ke Malam Fatori a jihar Borno.
Ali ya jagoranci daya daga cikin gagarumin artabun da sojin Najeriya suka yi da Boko Haram a watan Fabrairun 2015, wanda hakan yasa suka kwace garin Baga a Borno.
Asali: Legit.ng