Boko Haram sun gurgunta mulki a Neja, sun kayyade shekarun aurar da 'ya'ya mata
- 'Yan ta'addan Boko Haram sun kwace mulki a wasu yankunan jihar Neja inda suka koma hukuma baki daya
- 'Yan Boko Haram sun tattara jama'ar yankin inda suka kayyade wa iyaye cewa a shekaru 12 za su dinga aurar da yara mata
- An gano cewa, a Awulo, Kuregbe da Kawure, 'yan ta'addan ne ake kai wa kara ko da kuwa rikicin cikin gida ne sai su yi sasanci
Shiroro, Niger - 'Yan ta'addan Boko Haram sun addabi jama'a mazauna karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja da su dinga aurar da 'ya'yansu mata a shekaru 12.
Daily Trust ta ruwaito cewa, mazauna yankin da lamarin ya shafa sun ce 'yan ta'addan sun ba su umarnin cewa kada su kuskura su saurari wata hukuma.
Daya daga cikin mazauna yankin kuma daga cikin matasan Shiroro mai suna Bello Ibrahim, ya sanar da Daily Trust cewa:
"A wani lokaci, suna kauyen Kawure, kauyen tsohon sanata mai wakiltar Niger ta gabas, David Umaru.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Amma dakarun soji sun fatattake su bayan ayyukan rundunar hadin guiwa. Sai dai kuma, bayan wani lokaci, sun sake komawa saboda babu sansanin soji a wurin.
"Toh a yanzu, ba a Kawure kadai su ke ba, sun bazu har zuwa yankunan da suka hada da Kuregbe, Awulo da sauransu.
“A Awulo da kuma yankin Kuregbe, sun tattaro jama'a Musulmi da Kirista kuma sun ba su umarnin aurar da 'ya'yansu mata a shekaru 12.
"Babu wata doka a yankin baya da ta Boko Haram. Idan mazauna yankin suna da wata matsala ko da ko ta cikin gida ce, su ake kai wa kara domin sasanci.
"Babu wani korafi da ake kai wa 'yan sanda ko kotu ko kuma wata hukuma domin sasanci."
Wani mazaunin yankin ya ce 'yan ta'addan na rayuwarsu a sake. A cewarsa:
"Suna al'amuran rayuwarsu kamar kowa kuma a sake suke rayuwa da 'yan kauyen. Sun zama hukuma a kauyukan. A Kawure, Awulo da Kuregbe ne suka da sansanoninsu. Su na tirsasa mazauna yankunan wurin yi musu biyayya.
"A dukkan gundumomin Chukuba da Kuregbe, babu wasu 'yan fashin daji, 'yan Boko Haram ne zalla."
Shugaban karamar hukumar Shiroro, Suleiman Chukuba ya tabbatar da tururuwar da 'yan Boko Haram ke yi a yankin. Ya ce gundumomi hudu ne lamarin ya shafa.
DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016
A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta karrama Muhammad Abu Ali, soja mai mukamin laftanal kanal kuma kwamandan bataliya ta 272 a baya wanda Boko Haram suka kashe a 2016.
TheCable ta ruwaito cewa, a ranar 4 ga watan Nuwamban 2016, 'yan ta'addan Boko Haram sun halaka Ali yayin da suka kai wa bataliya ta 119 farmaki da ke Malam Fatori a jihar Borno.
Ali ya jagoranci daya daga cikin gagarumin artabun da sojin Najeriya suka yi da Boko Haram a watan Fabrairun 2015, wanda hakan yasa suka kwace garin Baga a Borno.
Asali: Legit.ng