Da duminsa: Dan majalisar tarayya ke daukar nauyin Sunday Igboho da Nnamdi Kanu, Buhari ya yi ikirari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wanda ke daukar nauyin masu fafutukar ganin an raba kasar
- A yayin jawabinsa na ranar 'yancin kasa karo na 61, shugaban kasar ya ce akwai dan majalisar tarayya cikin masu daukar dawainiyar masu fafutukar
- Buhari ya ce an gano hakan ne yayin gudanar da bincike bayan kama Nnamdi Kanu da Sunday Igboho
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ikirarin cewa wani dan majalisar tarayya ne ke da alhakin daukar nauyin masu kira-kirayen neman ballewar kasar nan.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga kasar a matsayin wani bangare na bikin ranar 'yancin kai.
Ya bayyana cewa an gano hakan ne yayin da ake gudanar da bincike bayan kamun Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar neman kasar Biyafara da kuma Sunday Igboho, shugaban masu fafutukar kasar Yarbawa.
Ya ce:
“Kamen da aka yi kwanan nan na Nnamdi Kanu da Sunday Adeyemo, da kuma binciken da ake gudanarwa ya nuna wasu manyan masu kudi ne a bayan wadannan mutane.
"Muna bin diddigin waɗannan masu daukar nauyin dawainiyarsu ta kudi ciki har da wanda aka bayyana a matsayin memba mai ci na Majalisar Dokoki ta ƙasa."
Buhari ya bada umurnin a buɗe wa 'yan Nigeria Twitter, amma da sharaɗi
A gefe guda, mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a, ya ce ya bada umurnin a dage dakatarwar da aka yi wa shafin Twitter a Nigeria tun watan Yunin 2021.
The Punch ta ruwaito cewa Buhari ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi wa 'yan Nigeria na ranar bikin samun 'yancin kasa karo na 61.
Ya bayyana cewa kafafen sada zumunta na da amfani amma ya koka kan yadda wasu ke amfani da kafar don shirya muggan ayyuka da watsa labaran karya da kabilanci da tada rikicin addini.
Asali: Legit.ng