Dr Pantami ya bukaci hukumomin tsaro su yi amfani da 5G wajen magance tsaro

Dr Pantami ya bukaci hukumomin tsaro su yi amfani da 5G wajen magance tsaro

  • Ministan sadarwa ta tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Pantami ya bayyana hanyar da gwamnai ke bi don magance tsaro
  • Ya ce, ya kamata hukumomin tsaro su yi amfani da 5G don magance matsalolin tsaro a Najeriya
  • Ya bayyana haka ne yayin da ya ke gabatar da jawabi a wani taro da hukumar NSCDC ta shirya

Abuja - Ya kamata hukumomin tsaro a Najeriya su yi amfani da hanyar sadarwa ta 5G da Gwamnatin Tarayya ta amince da dasawa don magance matsalar rashin tsaro, in ji Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami.

Ya fadi haka ne a Abuja ranar Talata yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi a taron tsaro da hukumar tsaro NSCDC ta shirya, mai taken; ‘Synergy: Panacea to Effective Critical Assets and Infrastructure Protection.’

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Gwamnatin Buhari ta bayyana burin amfani da 5G don magance rashin tsaro
Tirken sadarwar 5G | Hoto: nairametrics.com
Source: UGC

Ya ce:

“A wani bangare na kokarinmu na tabbatar da kariya ga mahimman kadarorin kasa, muna aiki tare da ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa don fito da wani Babban Tsari don tabbatar da cewa muhimman kadarorinmu na kasa, musamman a bangaren ICT sun kasance da kariya."

Ya ce gwamnati ta kafa cibiyoyin gaggawa na na'ura mai kwakwalwa guda uku don yakar laifuka a fadin kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce domin samun damar inganta bincike da ci gaba a wannan fanni, gwamnati ta kuma kafa wata cibiya da aka yi wa lakabi da 'National Centre for Artificial Intelligence and Robotics (NCAIR)'.

Majalisar dattawa ta bayyana burinta kan sabis na 5G, ta ce NCC ta samar da N350bn

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Majalisar Dattawa ta nemi Hukumar Sadarwa ta Najeriya da ta yi amfani da tsarin sadarwa na 5G don samar wa Gwamnatin Tarayya kudin shiga N350bn a cikin kasafin kudi na shekarar 2022.

Idan baku manta ba, mun ruwaito muku cewa, gwamnatin tarayya ta amince a dasa tare da fara amfani tsarin sadarwar 5G a Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.

Wannan shi ne hukuncin kwamitocin hadin gwiwa na Majalisar Dattawa da ke aiki kan Tsarin Kudin Matsakaicin Shiri na 2022-2024, lokacin da gudanarwar Hukumar NCC ta bayyana a gaban kwamitin zauren majalisar.

Shugaban kwamitocin hadin gwiwa, Sanata Solomon Adeola, ya ce kasafin kudin 2022 na NCC ba zai zama N115bn ba, wanda shine adadin da ta yi hasashe.

Ana ta cece-kuce kan wutar Mambila, gwamnati ta fitar hotunan wutar Zungeru

A wani labarin, Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fitar da wasu hotuna a wani bangare na nuna wa 'yan Najeriya tana aikin tashar wutan lanatarki ta Zungeru dake jihar Neja.

Read also

Yadda kasar Ghana ke damfarar ‘yan Najeriya ta hanyar Korona, 'yan majalisa

A baya, gwamnatin Najeriya ta fara aikin tashar ne tun a shekarar 2013, inda ta nufi kammala aikin a shekarar 2018 wanda kuma hakan bai samu ba, wannan yasa a ka sake sanya watan Disambar 2021 a matsayin lokacin da za a kammala aikin, kamar yadda Wikipedia ta tattaro.

Legit.ng Hausa kafar yanar gizo ta Afrik 21 ta ce an ware makudan kudaden da suka kai dalolin Amurka biliyan 1.3 don wannan aiki.

Source: Legit

Online view pixel