Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

  • Jami'an tsaron jami'ar Maiduguri sun kutsa har cikin dakunan kwanan dalibai mata inda suka cafko masu zanga-zanga kan karin kudin makaranta
  • An gano cewa, daruruwan dalibai mata ne suka fita zanga-zanga amma sai jami'an tsaron suka dinga dukansu tare da amfani da karfi wurin hana su
  • Bayan cafke wasu daga ciki, sun kara da zuwa har dakunansu inda suka kamo wasu tare da yi musu fatali da kayansu a farfajiyar rukunin dakunansu

Maiduguri, Borno - Wani bidiyo ya bayyana inda ya ke nuna yadda jami'an tsaron jami'ar Maiduguri, UNIMAID, suka cafke dalibai mata 38 har cikin dakunan kwanansu da ke makarantar.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, daliban da aka kama suna daga cikin wadanda suka yi zanga-zanga kan karin kudin makaranta da kuma halin da suke ciki a jami'ar.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda Bagudu ya wawuri biliyoyi tare da boyesu a ketare tun zamanin Abacha

Daruruwan dalibai mata na jami'ar UNIMAID sun yi gangami a ranar Litinin inda suka balle zanga-zangar lumana, amma karfa-karfan da jami'an tsaro suka nuna musu yasa suka hakura da zanga-zangan.

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga
Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Jami'an tsaro sun yi amfani da tsananin karfinsu wurin hana daliban aiwatar da abinda suka yi niyya.

Da yawa daga cikin dalibai matan sun dinga gudun neman wurin tsira inda a hakan suka samu raunika, yayin da jami'an tsaron suka dinga dukan wasu da sanduna, Daily Nigerian ta wallafa.

A kalla goma sha takwas daga cikin daliban masu zanga-zanga aka kama tare da garkame su a ofishin jami'an tsaro cikin mawuyacin hali har zuwa safiyar Talata.

"A ranar Talata, jami'an tsaron sun sake tsinkayar wasu dakunan daliban mata inda suka damke sama da dalibai ashirin," wata majiya ta sanar wa PRNigeria.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun gurgunta mulki a Neja, sun kayyade shekarun aurar da 'ya'ya mata

"Wadanda aka gane sun yi zanga-zangar aka sake kwashewa daga dakunan kwanansu kuma aka watsar da kayan su a farfajiyar rukunin dakunan yayin da aka kwace katikan shaidar dalibtarsu," wani dalibi yace.

Farfesa A. M. Gimba, shugaban bangaren kula da al'amuran daliban makarantar, tun farko ya ja kunnen cewa hukumar makaranta za ta matukar sabawa duk wanda yayi yunkurin yin karantsaye ga zaman lafiyan makarantar.

Gimba wanda ya bada jan kunnen ta wata takarda da ya fitar a ranar Talata, ya ce UNIMAID ba za ta lamunci duk wata dabi'a mara kyau ba daga dalibai ko masu kutse da suka zo tabarbara tsarin makarantar.

Fallasar handama: An matsa wa Buhari lamba kan ya bincike Bagudu, Obi da sauransu

A wani labari na daban, ana cigaba da matsanta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari lamba kan ya binciki daya daga cikin makusantansa, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da dukkan 'yan Najeriya da bincike ya bayyana sun adana kazamar dukiya a duniya.

Kara karanta wannan

Ta fashe: Sirrin kazamar dukiyar shugabannin duniya 35, 'yan siyasa 330 da biloniyoyi 130 a kasashe 91

Takardun Pandora da aka saki a wannan makon ya fallasa sirrin kazamar dukiyar wasu shugabannin duniya, 'yan siyasa da biloniyoyi da suka hada da masu fadi a ji a Najeriya.

Baya da Bagudu da Obi, akwai tsohon babban alkalin Najeriya, 'yan majalisa masu ci yanzu da tsoffin 'yan majalisa, fasto da kuma wasu manya a kasar nan da aka gano da hannu cikin satar kudade tare da boye kadarori a kasashen ketare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel