Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

  • Tsohon saurayi ya haddasa mutuwar auren tsohuwar budurwarsa a daren daurin aurenta
  • Ango kuwa ya mikawa Amaryar takardar saki ana cikin shagalin biki
  • Amaryar tace ta yi watsi da tsohon saurayin ne saboda ta gano basu dace da juna ba

Saudiyya - A daren farko ya mutu yayinda ake tsakiyar shagalin biki lokacin da Ango ya smau sakon hotunan Amaryarsa na irin lalatan da tayi a shekarun baya kafin su hadu.

Shafin LISA ya ruwaito cewa ngon ya samu wasika tattare da katin Memory da wani ya turo yana zargin Amaryar da kasance mutuniyar banza.

Hakan ya sa Angon ya hanzarta wajen kallon abinda ke cikin Memorin.

Ya shige cikin daki shi kadai don gani

Ango ya shiga daki idan ya gano wani tsohon saurayinta ne ya aiko da sakon cike da hotunansu na da suna badala.

Kara karanta wannan

A tura matasan NYSC faggen yaki da yan bindiga, wanda ba zai je ba a daina biyansa albashi

Wannan abu bai yiwa angon dadi ba kuma take ya yanke shawarar kawo karshen shagalin da ake yi.

Kai tsaye Angon ta danna mata saki.

Tsohon Saurayin Amarya ya aikewa sabon angonta hotunanta na lalata, aure ya mutu a daren farko
Tsohon Saurayin Amarya ya aikewa sabon angonta hotunanta na lalata, aure ya mutu a daren farko
Asali: UGC

Amaryar ta yi tsokaci kan lamarin

Daga baya Amaryar ta bayyana cewa lallai sun yi soyayya da tsohon saurayin amma daga baya suka fahimci cewa basu dace da juna ba. Sai ta yanke shawarar watsi da shi tunda iyayenta sun sama mata sabon saurayin da ya dace da ita.

Tsohon Saurayin ya bukaci ta ziyarcesa ana gab da aure

Ta kara da cewa tsohon saurayin ya bukaci ta kawo ziyara gidansa ana sauran yan kwanaki da aure amma tayi banza da shi.

Ta ce ba ta son ta sake maimaita irin kura-kuran da tayi a baya saboda tana son fara sabuwar rayuwa da mijinta.

Kara karanta wannan

Me ya yi zafi: Saurayi ya bi buduwarsa har wurin alibidi ya buɗe wa baƙi wuta da bindigarsa

Ashe wannan abu bai yiwa tsohon saurayin dadi ba inda ya fara dura mata ashariya kuma yayi alkawarin tona mata asiri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel