Ana ta cece-kuce kan wutar Mambila, gwamnati ta fitar hotunan wutar Zungeru

Ana ta cece-kuce kan wutar Mambila, gwamnati ta fitar hotunan wutar Zungeru

  • Yayin da ake ci gaba da fuskantar karshen 2021, gwamnatin Buhari ta fitar da hotunan aikin wutan lantarki na Zungeru
  • An watsa wasu hotuna a kafafen sada zumunta da ke nuni da aikin tashar wutan lantarkin ya jima da yin nisa
  • Wannan na zuwa ne bayan da bincike ya nuna gwamnatin tarayya ba ta fara aikin komai na tashar wutan Mambila ba

Abuja - Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fitar da wasu hotuna a wani bangare na nuna wa 'yan Najeriya tana aikin tashar wutan lanatarki ta Zungeru dake jihar Neja.

A baya, gwamnatin Najeriya ta fara aikin tashar ne tun a shekarar 2013, inda ta nufi kammala aikin a shekarar 2018 wanda kuma hakan bai samu ba, wannan yasa a ka sake sanya watan Disambar 2021 a matsayin lokacin da za a kammala aikin, kamar yadda Wikipedia ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Legit.ng Hausa kafar yanar gizo ta Afrik 21 ta ce an ware makudan kudaden da suka kai dalolin Amurka biliyan 1.3 don wannan aiki.

Yayin da ake cece-kuce kan batun wutar Mambila, gwamnati ta fitar hotunan wutar Zungeru
Hotunan tashar wutar | Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

A wasu hotuna da wani hadimin shugaba Buhari ta fannin yada labarai Bashir Ahmad, ya fitar ta shafinsa na Facebook yau Talata 28 ga watan Satumba, an ga wuraren da ake aikin, tare da nuna alamun lallai aikin ya yi nisa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rubutunsa, Bashir ya ce:

"Tashar Wutar Lantarki ta Zungeru ita ce tashar wutar lantarki mai karfin megawatt 700 (940,000 hp) da ake ginawa. Idan aka kammala ta, za ta zama tashar wutar lantarki ta biyu mafi girma a kasar, bayan Tashar Wutar Lantarki ta Kainji mai karfin megawatts 760 (1,020,000 hp)."

Kalli hotunan:

A bangare guda, an samu shakku da jimami hade da kaduwa yayin da wani binciken BBC ya bankado yadda gwamnati ta yi ikrarin gudanar da aikin tashar wutan lantarki a Mambila, wanda aka gano ba a fara komai ba.

Kara karanta wannan

Bikin 'yancin kai: FG ta tsaurara matakan tsaro, za ta rufe sakatariya a ranar Alhamis 30 ga wata

Mutane da dama sun bayyana kokensu da kuma yin Allah wadai da abin da suka kira yaudara daga gwamnatin tarayya.

Buhari da hannunsa ya bani lambar waya muna gaisawa amma bai tsinana min komai ba

A wani labarin, wani dan Najeriya ya bayyana kokensa ga shugaba Buhari, inda ya ce shugaban bai masa komai duk da cewa ya sha wahala wajen yakin neman zaben shugaban kasa.

Mutumin, wanda ya bayyana sunansa da Badamasi Sima Memai ya bayyana a cikin wani bidiyon da ya yi yawo a kafar sada zumunta ta Facebook a shafin Nasara Radio 98.5 FM, inda ya ke nuna rashin jin dadinsa da halin da Najeriya ke ciki.

Badamasi ya bayyana irin wahalar da ya sha da shi da ire-irensa basu kaunar shugaba Buhari lokacin yakin neman zabe, inda ya ce sun jure watsa musu ruwan zafi da aka yi amma basu saduda akan shugaban ba.

Kara karanta wannan

Yadda ni da Sanusi II muka rike darajar Naira na tsawon shekara 5 a CBN inji Farfesa Moghalu

Asali: Legit.ng

Online view pixel