Yadda kasar Ghana ke damfarar ‘yan Najeriya ta hanyar Korona, 'yan majalisa

Yadda kasar Ghana ke damfarar ‘yan Najeriya ta hanyar Korona, 'yan majalisa

  • Majalisar wakilai ta nuna damuwa kan yadda wasu bata-gari ke samar da sakamakon rigakafin Korona na karya
  • Wannan lamari na faruwa ne a kasar Ghana yayin da kasar ke sanya 'yan Najeriya biyan makudan kudade don killace
  • Majalisar ta bayyana bukatar daukar matakin gaggawa don magance wannan matsala da ta kunno kai

Abuja - Rahoton da Daily Trust ta fitar ya ce, 'yan majalisar tarayya sun yi gargadin cewa ana amfani da sakamakon gwajin Korona na karya don damfarar 'yan Najeriya a kasar Ghana.

Sanata Ibrahim Oloriegbe (APC, Kwara) ya tayar da batun ne a cikin kudirin da sanata Sadiq Umar (APC, Kwara), Betty Apiafi (PDP, Ribas) da Chukwuka Utazi (PDP, Enugu) suka gabatar.

Yayin gabatar da kudirin, Oloriegbe ya lura cewa akwai alamar ayar tambaya cewa 'yan Najeriya da aka gwada aka ga lafiyarsu a cikin kasar sun kamu da Korona a Ghana.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Yadda kasar Ghana ke damfarar ‘yan Najeriya da gwajin Korona na bogi, 'yan majalisa
Majalisar Wakilai ta Najeriya | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Twitter

Ya ci gaba da cewa hukumomin Ghana galibi suna yiwa ‘yan Najeriya da ke ziyartar kasar killacewa na tsawon makonni biyu kuma ana sanya su biyan kusan N70,000 a kowace rana.

A cewar dan majalisar, 'yan Najeriya da ke tafiya Ghana ko masu wucewa ta Ghana sun koka da yadda ake sanya su biyan kusan Naira miliyan daya yayin da suke kebe.

Ya ce idan ba a binciki zargin da kyau ba kuma ba a magance shi ba, za a ci gaba da barnar, ta haka ne za a kwace dukiyar 'yan Najeriya ba bisa ka'ida ba a yayin da ake fuskantar kalubalen tattalin arziki a duniya.

Oloriegbe ya kuma lura cewa:

"Akwai matukar bukatar ci gaba da neman allurar rigakafi da sakamakon gwaji saboda manyan 'yanci da za su baiwa mutane.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

"Hakanan, ko yaushe ana iya samun mutanen da ba sa son jira allurar rigakafin su a hukumance, ko kuma sakamakon gwaji a hukumance .kuma mutane da ke cikin bukata na iya fadawa cikin wannan lamarin.2

Ya nuna damuwar sa cewa:

"Idan ba a magance zargin mutane na samun da yin amfani da katunan rigakafin Korona na karya don yin balaguro ba, yana iya haifar da mummunan sakamako ga 'yan Najeriya masu katunan rigakafin Korona na gaske daga balaguro zuwa kasar waje."

Don haka, Majalisar Dattawa ta umarci kwamitocin ta kan Lafiya da su gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen biyu na sakamakon gwajin Korona na karya da ake amfani da su don damfarar 'yan Najeriya a Ghana da tsarin samun katunan rigakafin Korona na karya.

Gwamnatin Buhari ta fara bin coci don yiwa masu bautar ranar Lahadi riga-kafin Korona

Gwamnatin tarayya a ranar Talata 14 ga watan Satumba ta sanar da shirinta na daukar allurar riga-kafin Korona zuwa cibiyoyin bauta ta Kiristoci, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai farmaki coci, sun sheke mai bauta

Babban Darakta na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko, Faisal Shuaib, ya bayyana hakan ne yayin wayar da kan shugabannin Kiristoci kan kashi na biyu na riga-kafin Korona a babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce:

“Mai martaba, Shugaban CAN, fitattun shugabannin Kirista, mata da maza, ina mai farin cikin sanar da ku cewa daga wannan mataki na 2 na riga-kafin Korona, mun gabatar da allurar riga-kafin ranar Lahadi."

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

A wani labarin na daban, Babban limamin masallacin Juma’a na Apo Legislative Quarters dake Abuja, Sheikh Muhammad Khalid, kwanan nan ya yi fice a kafafen sada zumunta bayan faifan bidiyon wa’azin sa da ya soki shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya bazu.

A cikin wata hirar da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar Punch, malamin addinin Islaman ya ce yana tsaye kan kalamansa cewa shugaban bai tsinana komai ba.

Kara karanta wannan

Bayan kai karar mahaifiyarsa ga EFCC, dan Ganduje ya tsere zuwa Egypt

A tattaunawar, malamin ya bayyana abubuwan da suke damunsa game da gwamnatin shugaba Buhari, wadanda a cewarsa gwamnatin ta cika yiwa 'yan Najeriya karerayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel