Gwamna Zulum ya dakatar da shugabannin makarantar da ya yi karatu yayin da ya kai ziyarar bazata

Gwamna Zulum ya dakatar da shugabannin makarantar da ya yi karatu yayin da ya kai ziyarar bazata

  • Gwamnan jihar Borno, ya dakatar da shugabannin makarantar kimiyya ta Ramat da ke Maiduguri, na tsawon watanni shida
  • Zulum ya dauki wannan mataki ne sakamakon gani da yayi komai na makarantar ya mutu murus a yayin da ya kai ziyarar bazata
  • Ya kuma umurci kwamishinan ilimi na jihar, Dr. Babagana Mallumbe, da ya karbi ragamar harkokin Makarantar nan take sannan ya saisaita abubuwa cikin gaggawa

Gwamna Babagana Zulum ya dakatar da dukkanin shugabannin kwalejin kimiyya ta Ramat da ke Maiduguri, na tsawon watanni shida.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Zulum ya kasance dalibin kwalejin kimiyyar daga shekarar 1986 zuwa 1988. Ya sami difloma a bangaren Injinyan Noma kafin ya koma makarantar a matsayin shugaba daga 2011 zuwa 2015.

Kara karanta wannan

Masu neman kujerar sarkin Kwantagora sun yi watsi da sakamakon zabe, sun nemi a sake sabo

A yayin ziyarar bazata da ya kai, gwamnan ya yi mamakin ganin cewa dakunan bitar aiki da na gwaje-gwaje ba sa aiki, yayin da ‘makarantar ta mutu murus’.

Gwamna Zulum ya dakatar da shugabannin makarantar da ya yi karatu yayin da ya kai ziyarar bazata
Gwamna Zulum ya dakatar da shugabannin makarantar da ya yi karatu yayin da ya kai ziyarar bazata Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Gwamnan ya ziyarci makarantar da misalin ƙarfe 9:00 na safe sannan ya gano cewa ba a amfani da yawancin dakunan gwaje-gwajen, inda ya-na suka rufe wasun su sannan ga beraye suna yawo saboda rashin kulawa.

Bayan tantance wurin, Zulum ya umarci kwamishinan manyan makarantu, kimiyya, fasaha da kirkire -kirkire na jihar, Dr. Babagana Mallumbe, da ya karbi ragamar harkokin Makarantar nan take, Daily Trust ta kuma ruwaitowa.

Ya ce:

“Ni a iya sanina, wannan Kwalejin ta mutu. Babu abin da ke aiki. Dakunan bitar aiki sun tashi aiki, dakin bitar aikin gona ba ya aiki, haka nan cibiyar koyon sana’a ba ya aiki.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa

“Makarantar tana fuskantar dubban matsaloli, kama daga rashin kudi da jajircewa. A matsayina na tsohon ɗalibin wannan kwalejin, tsohon shugaba, ina da riko da ɗabi'a a wannan kwalejin. Insha’Allah, ba zan bari wannan kwaleji na kimiyya ta lalace a lokacin da nake a matsayin Gwamnan Jihar Borno ba. Zan yi duk abin da zan iya don tabbatar da aikin wannan cibiya insha Allah.
“Na umarci Kwamishinan Ilimi da ya karbi ragamar harkokin makarantar na watanni shida masu zuwa. Ma'aikatar ta tabbatar da ganin cewa an dawo da dukkan bita da dakunan gwaje -gwaje bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.
“Sannan a gaggauta dawo da cibiyar koyon sana’a don amfani da ita. Lokacin da nake a matsayin shugabar makarantar, cibiyar koyon sana’a tana samar da akalla teburi da kujeru 10,000 zuwa 20,000 kowane wata. Mun samar da gadajen asibiti.”

Gwamnan ya yi ganawar sirri tare da manyan manajojin Kwalejin.

Kara karanta wannan

Yarimomi 45 sun shiga jerin masu neman mulkin Sarkin Sudan na Kontagora

Zulum ya kori NGO mai suna ACTED bayan an kama su suna koyar da harbi a Maiduguri

A wani labari na daban, mun ji a baya cewa Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bada umarnin dakatar da wata kungiyar taimako ta kasar waje mai suna ACTED bayan bankado cewa suna koyar da jama'a harbi a wani otal dake Maiduguri.

Mai magana da yawun Zulum, Isa Gusau, ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook inda ya sanar da umarnin gwamnan tare da cewa kungiyar ta asalin Faransa an kamata ne da bindigogin wasa kuma tana koyar da harbi a Maiduguri.

Gusau yayi bayanin cewa mazauna kusa da otal din sun kaiwa jami'ai rahoton cewa suna jin harbin bindiga daga otal, lamarin da yasa jami'an gwamnati suka kai kara ofishin 'yan sandan har aka tattaro aka zo duba otal din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel