Masu neman kujerar sarkin Kwantagora sun yi watsi da sakamakon zabe, sun nemi a sake sabo
- Wasu daga cikin masu neman sarautar Sarkin Sudan na Kwantagora a Jihar Neja sun yi watsi da sakamakon zaben sabon sarkin
- Sun nemi a sake sabon zabe bisa zargin cewa an yi magudi don fifita wani dan takara da aka fi so
- Daya daga cikin yan takarar ya zargi kwamitin zaben da kuma Ma’aikatar Kananan Hukumomin da kauce ka’ida yayin aikin
Kontagora, Neja- Wasu daga cikin masu fafutukar neman maye gurbin marigayi sarkin Kontagora sun yi watsi da sakamakon zaben, inda suka yi zargin cewa an yi magudi don fifita wani dan takara da aka fi so, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
An tattaro cewa kimanin mutane 47 ne suka nuna sha’awarsu ta son zama Sarkin Sudan na Kontagora.
Gagarumin sako zuwa Kudu maso Gabas: Ku rungumi APC ko ku rasa dama a 2023, Tsohon dan majalisa yayi gargadi
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu a Jihar Neja, Barista Abdulmalik Sarkin Daji ya sanar da sakamakon zaben sarautar Kontagora da aka yi a ranar Lahadi.
Kwamishinan, wanda ya sanar da haka ta gidan rediyon Landmark FM Kontagora, ya ce Mohammed Barau ne ya samu mafi yawan kuri'u amma gwamna Abubakar Sani Bello na da ikon da doka ta bashi na zabar sarki na gaba daga cikin manyan ‘yan takara.
Sai dai, daya daga cikin masu takarar, Barista Mika Anache, a ranar Litinin ya yi kira da a soke shirin, inda ya zargi kwamitin zaben da ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu da cin zarafin ka’idojin zaben.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta umarci masu zaben sarki da su gudanar da sabon zabe tare da cire kwamishinan kananan hukumomi saboda zargin "rashin iya aiki da rashin iya gudanar da al'amuran masarautar Kontagora."
Mai karar ya kuma aike da kwafin korafin ga Kakakin Majalisar Dokokin Jihar da Etsu Nupe da shugaban DSS da tsoffin Shugabannin Kasa Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar da kuma shugaban masu zaben sarkin na masarautar, Alhaji Shehu Yusuf Galadima.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa Barista Anache ya zargi masu zaben sarki da ma'aikatar da hana masu takarar shiga wurin zaben.
Ya kuma ce ba a bi tsarin da ya dace ba wajen zaben sannan kuma ya saba ka'idojin da gwamnatin jihar ta bayar ga masu zaben sarkin.
Ya ce kwamitin zaben ya yi jinkiri wajen sanar da sakamakon zaben da ya kamata a sanar a wurin da aka gudanar da shi.
Sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, dukkan wadanda aka mika wa kwafin takardar korafin ba su kai ga mayar da martani a kai ba.
Yarimomi 45 sun shiga jerin masu neman mulkin Sarkin Sudan na Kontagora
A baya Legit.ng ta rahoto cewa akalla Yarimomi 45 kawo yanzu sun bayyana niyyar na ahwa karagar mulkin Sarkin Sudan na Kontagora.
Wannan ya biyo bayan rasuwar Sarkin Kontagora, Alhaji Said Umaru Namaska, wanda ya rasu bayan shekaru 47 kan mulkin.
Daily Trust ta ruwaito cewa kawo yanzu, mutum 21 cikin wadanda suka dauki takardar takara sun kammala cikawa kuma sun dawo da shi.
Asali: Legit.ng