Zulum ya kori NGO mai suna ACTED bayan an kama su suna koyar da harbi a Maiduguri

Zulum ya kori NGO mai suna ACTED bayan an kama su suna koyar da harbi a Maiduguri

  • Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya dakatar da wata NGO mai suna ACTED bayan kamata tana koyar da harbi
  • Mazauna kusa da wani otal a Maiduguri suna kai korafin jin harbi da suke yi inda 'yan sanda suka hanzarta zuwa
  • Sun kama wasu mutum 2 suna koyar da harbi da bindigogin roba kuma an gano kungiyar taimakon ta asalin Faransa ce

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bada umarnin dakatar da wata kungiyar taimako ta kasar waje mai suna ACTED bayan bankado cewa suna koyar da jama'a harbi a wani otal dake Maiduguri.

Mai magana da yawun Zulum, Isa Gusau, ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook inda ya sanar da umarnin gwamnan tare da cewa kungiyar ta asalin Faransa an kamata ne da bindigogin wasa kuma tana koyar da harbi a Maiduguri.

KU KARANTA: Gwamnatin Borno ta dauka mataki kan dakatar da dalibai saboda basu tari Buhari ba

Zulum ya kori NGO mai suna ACTED bayan an kama su suna koyar da harbi a Maiduguri
Zulum ya kori NGO mai suna ACTED bayan an kama su suna koyar da harbi a Maiduguri. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyon saurayin da ya baiwa budurwa kyautar N2.5m saboda ta amince zata aure shi

Gusau yayi bayanin cewa mazauna kusa da otal din sun kaiwa jami'ai rahoton cewa suna jin harbin bindiga daga otal, lamarin da yasa jami'an gwamnati suka kai kara ofishin 'yan sandan har aka tattaro aka zo duba otal din.

'Yan sandan sun samu wasu bindigogin roba na fiston tare da wasu mutum biyu masu horarwan, akwai dan Najeriya daya a cikinsu kuma a halin yanzu suna wurin 'yan sandan domin bincike.

Takardar tace an dakatar dasu a halin yanzu kafin 'yan sandan su kammala bincike kuma Zulum ya bada umarnin garkame otal din tare da dakatar da suk wasu ayyukan ACTED a jihar Borno.

Gusau yace Zulum yana godiya ga dukkan kungiyoyin taimako dake samar da kayan tallafi a sassan jihar Borno.

A wani labari na daban, fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Gumi, ya ce shiga daji da yake yi domin tattaunawa da 'yan bindiga duk yana yi ne da hadin guiwar hukumomin gwamnati da cibiyoyin tsaro.

Gumi ya tabbatar da cewa bai taba yin wani laifi ba in dai batun shiga daji ne domin tattaunawa da 'yan bindiga, Channels TV ta ruwaito.

Ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 25 ga watan Yuni bayan kammala sallar Juma'a a masallacin Sultan Bello dake jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel