'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa

'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa

  • Mai Magana da yawun rundunar sojin kasa ya ankarar da jama'a kan gangamin diban aiki da miyagun ISWAP ke yi
  • Onyema Nwachukwu ya ce kungiyar ta'addancin ta matukar girgiza sakamakon tuban da mambobinsu ke yi
  • Ya sanar da hakan yayin rangadin da ya je Maiduguri inda ya ce kafafen sada zumunta sun taimaka da wayar da kai

Borno - Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar sojin kasa ta Najeriya, ya ce 'yan ta'addan ISWAP sun fara gagarumin gangamin diban jama'a domin zama mambobinsu.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, rundunar sojin ta kaddamar da hare-hare kan miyagun 'yan ta'addan karkashin Operation Hadin Kai a yankin arewa maso gabasa ta kasar nan.

'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa
'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa. Hoto daga Thecable.ng
Asali: Facebook

Daruruwan 'yan ta'adda da suka hada da manyan kwamandojinsu sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a makonni kalilan da suka gabata.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun halaka rai 1, sun yi garkuwa da wasu a Sokoto

A yayin zagayen rundunar Hadin Kai a Maiduguri, jihar Borno a ranar Lahadi, Nwachukwu ya yi kira ga masu yada labarai da su taimaka wurin toshe duk wata kafar yaudarar jama'a su shiga kungiyar.

TheCable ta ruwaito cewa, ya kara da kira ga jama'a da su tabbatar da sun saka ido a yankunansu domin guje wa bata-gari.

"Zan so in sanar muku da cewa, miyagun ISWAP sun matukar girgiza a kwanakin nan sakamakon yadda mambobinsu ke mika wuya. Hakazalika, rikici na ta ballewa tsakaninsu," yace.
"Sun fara abinda muke kira da gagarumin gangamin daukan aiki kuma mun san cewa akwai matukar amfani idan kafafen sada zumunta za su toshe wannan kafar.
"'Yan ta'addan Boko Haram suna ta tuba tare da mika wuya. Jama'a suna ta tambayar ingancin tubansu kuma da dalilin da yasa suke tuba a wannan lokacin.

Kara karanta wannan

Daga bisani, NAF ta dauka alhakin yi wa farar hula ruwan wuta a Yobe

“Akwai kuma tambayoyi kan hadin kan wadannan miyagun. Wata tambaya kuma ita ce rudanin da wadanda lamarin ya ritsa da su.
“Wannan shi ne amfanin zagayen nan. Rundunar sojin ba zaune ta ke ba, ta dage wurin yaki da 'yan ta'adda da kuma rashin tsaron da ya addabi kasar nan."

Ya ce, akwai lokacin da 'yan ta'adda suka kusan kwace manyan biranen jihohin Adamawa, Borno da Yobe kuma suna karatowa wurin babban birnin tarayya Abauja. Amma a yanzu wannan ya zama tarihi domin an tsare su a Timbuks.

'Yan bindiga sun sheke rayuka 5, sun raunata wasu 5 a Kebbi

A wani labari na daban, miyagun 'yan bindiga sun halaka rayuka biyar tare da barin wasu biyar da miyagun raunika a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi, Daily Trust ta tattaro.

'Yan bindigan sun tsinkayi kauyen Uchukku a sa'o'in farko na ranar Juma'a, sun sace shanu tare da harbe mutum 5 har lahira.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta gargadi Yarbawa kan hada kai da kungiyoyin ta'addanci

Wani mazaunin Shanga mai suna Yushau Garba Shanga, ya sanar da Daily Trust cewa, 'yan bindigan sun kai farmaki wurin karfe 1:50 na dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel