Yarimomi 45 sun shiga jerin masu neman mulkin Sarkin Sudan na Kontagora

Yarimomi 45 sun shiga jerin masu neman mulkin Sarkin Sudan na Kontagora

  • An fara shirin nada sabon Sarkin Sudan na Masarautar Kontagora a jihar Neja
  • Sarkin Sudan ya rasu ne ranar 9 ga Satumba 2021
  • Ana zargin daya daga cikin yan kwamitin zaben sarki da rashin gaskiya, yayi murabus

Niger - Akalla Yarimomi 45 kawo yanzu sun bayyana niyyar na ahwa karagar mulkin Sarkin Sudan na Kontagora.

Wannan ya biyo bayan rasuwar Sarkin Kontagora, Alhaji Said Umaru Namaska, wanda ya rasu bayan shekaru 47 kan mulkin.

Daily Trust ta ruwaito cewa kawo yanzu, mutum 21 cikin wadanda suka dauki takardar takara sun kammala cikawa kuma sun dawo da shi.

Shugaban kwamitin zaben Sarki, Alhaji Shehu Galadima, ya bayyanawa manema labarai cewa mambobin kwamitinsa zasu tabbatar da cewa an yi zaben gaskiya da lumana.

Yace:

"Muna addu'a, kuma zamu tabbatar da cewa an kafa tarihi da wannan zabe. Mun lashi takobin yin adalci bisa ka'idojin zaben domin tabbatar ba'ayi son kai ba."

Kara karanta wannan

An saki bidiyo yayin da kwamandan IPOB/ESN Shakiti-Bobo ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin

Yarimomi 45 sun shiga jerin masu neman mulkin Sarkin Sudan na Kontagora
Yarimomi 45 sun shiga jerin masu neman mulkin Sarkin Sudan na Kontagora
Asali: UGC

Wani mamban dattawan masarautar, Manjo Janar Suleiman Saidu (mai ritaya) yace babu wanda zai samu fifiko wajen kwamitin zaben.

Yace:

"Kujerar Sarkin Sudan na Kontagora na daga cikin manyan kujerun sarauta a Arewacin Najeriya; saboda haka, ya kamata mu bi a hankali."
"Masu zaben Sarki subi ka'ida wajen zabe kamar yadda aka bukacesu."

Ana zargin daya daga cikin mambobin kwamitin zabe

Daya daga cikin mambobin kwamitin wanda shine Sakataren kwamitin, Ahmed Tijjani, ya yi murabus daga kujerar.

Wata majiya ta bayyana cewa ya yi murabus ne sakamakon kararraki da wasu yan takara suka shigar kansa a ma'aikatar kananan hukumomi.

Allah ya yiwa Sarkin Kontagora, Alhaji Saidu Umaru Namaska, rasuwa

Sarkin ya kwashe shekaru 47 kan mulkin Kontagora. Ya rasu yana mai shekaru 84.

Kara karanta wannan

Kwamandan NDA ya yi wa majalisa bayanin halin da ake ciki kan harin 'yan bindiga a NDA

Sarkin ya mutu kimanin watanni uku bayan kisan 'dansa, Yariman Kontagora. Gwamnan jihar Neja wanda yayi sanarwar ya nuna jimanin rashin Sarkin Kontagora.

A jawabin da Sakariyar yada labaransa, Mary Noel-Berje, ta saki, yace Sarkin ya bautawa al'ummarsa cikin gaskiya da adalci kuma za'a yi kewarsa sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng