Kwamandan NDA ya yi wa majalisa bayanin halin da ake ciki kan harin 'yan bindiga a NDA

Kwamandan NDA ya yi wa majalisa bayanin halin da ake ciki kan harin 'yan bindiga a NDA

  • Kwamandan makarantar NDA ya gana da kwamitin tsaro na majalisar wakilai kan batun harin NDA
  • A cewar kamfanin dillancin labarai na Najeriya, ganawar an yi ta cikin sirri ne ba tare da 'yan jarida ba
  • Kafin taron, a cewar NAN an bukaci dukkan manema labarai da su gaggauta barin wajen ganawar

Abuja - Kwamandan makarantar tsaro ta sojoji wato NDA, Ibrahim Yusuf, ya yi wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai bayani game da harin da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai makarantar.

A yayin harin a ranar 24 ga watan Agusta, an kashe jami’an soji guda biyu sannan an yi garkuwa da daya, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ba da rahoton cewa kwamandan ya gana da kwamitin ne cikin sirri, kamar yadda kwamandan ya ce an tsara takardun da za a gabatar wa membobin kwamitin.

Kara karanta wannan

2023: Shin Tinubu zai gaji Buhari? Sanannen sanatan arewa ya fede biri har wutsiya kan mulkin karba-karba

Kwamandan NDA ya yi wa majalisa bayanin halin da ake ciki kan harin 'yan bindiga a NDA
Majalisar wakilai a Najeriya | Hoto: dailytust.com
Asali: UGC

Mista Yusuf kafin taron ya shiga ganawar sirri, ya ce zai yiwa kwamitin bayani kan kokarin da sojoji ke yi na kubutar da jami'in da aka sace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa Babban Hafsan Tsaro, Lucky Irabor, ya ziyarci inda aka kai harin a ranar da abin ya faru, ya kara da cewa wasu manyan sojoji da ke aiki da wadanda suka yi ritaya su ma sun ziyarci wajen.

Don haka Shugaban Kwamitin, Babajimi Benson (APC-Lagos), ya nemi 'yan jarida da ke wurin da su fice, amma ya ce kwamitin zai bincika kan kokarin da ake yi na ceto jami'in da aka sace.

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce harin baya-bayan nan da aka kai Cibiyar Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA) a Kaduna zai taimaka wajen kara azama, kaimi da sa karfin soji wajen kawo karshen tashin hankali a kasar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka fasto a Kaduna, El-Rufai ya yi martani mai zafi

Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa:

"Wannan mummunan aikin zai hanzarta kawar da munanan abubuwan da ke faruwa, wanda membobin rundunar sojin suka kuduri aniyar aiwatarwa cikin kankanin lokaci."

A cikin wata sanarwa da daya daga cikin masu taimaka masa a bangaren yada labarai, Femi Adesina, ya ce, shugaban ya lura cewa mugun nufin da masu aikata laifuka ke yi don rage martabar sojojin kasar a idon duniya ya gaza.

Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da sojoji ke ragargazar masu tayar da kayar baya, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da sauran ire-iren masu aikata miyagun laifuka, musamman a arewa maso gabas.

Rundunar soja ta karyata zarginta da ake da son maida tubabbun Boko Haram sojoji

A wani labarin, Rundunar Sojin Najeriya ta ce ba za ta dauki tsoffin 'yan ta'adda masu tayar da kayar baya a cikin rundunar sojojin Najeriya ba, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Adamawa ya bayyana makudan kudaden da kowanne dan majalisa ke samu don ayyukan mazabu

Kakakin rundunar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata 24 ga watan Agusta a babban birnin tarayya Abuja.

Nwachukwu ya ce hankalin sojoji ya je ga wani bidiyo da wani matashi ya watsa a kafafen sada zumunta kuma Anthony Jay ya shirya wanda ya danganta rugujewar sojojin Afghanistan da mika wuya ga mayakan Boko Haram a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel