Rundunar soja ta karyata zarginta da ake da son maida tubabbun Boko Haram sojoji
- Rundunar sojin Najeriya ta karyata jita-jitar cewa rundunar za ta dauki tubabbun 'yan ta'addan Boko Harm
- Wannan na zuwa ne bayan da rundunar ta ce ta gano wani bidiyo dake nuna yunkurin hakan a kafafen sada zumunta
- Rundunar ta ce ba ta da niyyar daukar wasu tubabbun 'yan Boko Haram ta kowa ce fuska a kasar
Abuja - Rundunar Sojin Najeriya ta ce ba za ta dauki tsoffin 'yan ta'adda masu tayar da kayar baya a cikin rundunar sojojin Najeriya ba, The Cable ta ruwaito.
Kakakin rundunar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata 24 ga watan Agusta a babban birnin tarayya Abuja.
Nwachukwu ya ce hankalin sojoji ya je ga wani bidiyo da wani matashi ya watsa a kafafen sada zumunta kuma Anthony Jay ya shirya wanda ya danganta rugujewar sojojin Afghanistan da mika wuya ga mayakan Boko Haram a Najeriya.
Ya ce Young Elder, cikin raha, ya nuna damuwar sa game da maharan da suka mika wuya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Onyema:
"Duk da yake an fahimci cewa halin da ake ciki a Afghanistan abin damuwa ne ga duk wani mai tunani ko kungiya mai tunani, yadda Young Elder ya gabatar da hakan yana nuna karancin iliminsa kan batun da ya yi wa hawan kawara."
“Karancin ilimin da ke ciki ya haifar da wasu maganganu marasa tushe kuma marasa asali wadanda kawai ke cikin tunaninsu, suna masu cewa 'yan ta'adda da suka mika wuya za su shiga cikin Sojojin Najeriya.
“Don nisantar shakku, NA ba ta da wani dan ta’adda da ya tuba da zai shiga sahu kuma ba ta da wani shiri na yin hakan.
"Akwai 'yan Najeriya masu karfin gwiwa wadanda ke son shiga cikin NA don taimakawa da gaske wajen yakar ta'addanci da sauran manyan laifuka."
Lamari ya yi zafi: Dole mu nemo tsoffin sojoji don a yaki ta'addanci, inji CDS
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Lucky Irabor, ya ce Sojojin Najeriya za su nemo jami’an sojojin da suka yi ritaya don magance matsalar rashin tsaro a yankin arewa maso gabas.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata 24 ga watan Agusta a wani zaman tattaunawa na kwana daya tare da manyan jami’an da suka yi ritaya daga shiyyar arewa maso gabas da aka gudanar a runduna ta 23 da ke Yola, jihar Adamawa.
A jawaban da ya gabatar, Irabor ya ce:
“Yana daga cikin dalilin da ya sa nake nan tare da tawaga ta, don damawa da manyan abokan aikinmu da suka yi ritaya domin neman cikakkiyar mafita game da yadda za a kawo karshen rashin tsaro a yankin.
"Mun yi imanin cewa yayin da muke damawa da su, za su kasance a shirye don bude mana hanya a wuraren da za su inganta tsaro, kuma za su iya gaya mana wuraren da kuskuren mu ne don mu yi gyara."
Mambobin majalisa sun fashe da kuka saboda yawaitar harin 'yan bindiga
A wani labarin, 'Yan majalisar dokokin jihar Katsina biyu, a ranar Litinin, sun fashe da kuka a bayyane bisa yawan hare-haren da aka kai kwanan nan a cikin al'ummomin jihar ta Katsina, The Cable ta ruwaito.
Da yake magana ranar Litinin a zauren majalisar wanda kakakin majalisar Tasi’u Maigari ke jagoranta, Shehu Dalhatu-Tafoki, mataimakin kakakin majalisar, ya gabatar da wani kudiri na “mahimmantar da bukatar jama’a cikin gaggawa” kan matakin rashin tsaro a jihar.
A cewar Dalhatu-Tafoki, mamba mai wakiltar mazabar Faskari, duk da kokarin gwamnatin tarayya da na jihohi, da hukumomin tsaro, har yanzu al’ummomi na fuskantar hare-hare.
Asali: Legit.ng