Dan majalisar Adamawa ya bayyana makudan kudaden da kowanne dan majalisa ke samu don ayyukan mazabu

Dan majalisar Adamawa ya bayyana makudan kudaden da kowanne dan majalisa ke samu don ayyukan mazabu

  • Wani dan majalisar dokokin tarayya, Kwamoti Laori, ya ce kowane dan majalisar wakilai yana samun miliyan 100 don yin ayyukan mazabu
  • Sai dai, Laori ya ce shi da abokan aikinsa ba sa samun sama da miliyan 80 saboda rashin aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata
  • Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin da yake kaddamar da wasu ayyuka a mazabarsa a jihar Adamawa

Yola, jihar Adamawa - Kwamoti Laori, dan majalisar wakilai, ya ce kowane memba na majalisar yana samun kason Naira miliyan 100 don aiwatar da ayyuka a mazabun su.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, dan majalisar, yayi nadamar cewa saboda rashin aiwatar da kasafin kudi yadda ya kamata, 'yan majalisar da kyar suke samun sama da naira miliyan 80 daga cikin naira miliyan dari da aka ware.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

Dan majalisar Adamawa ya bayyana makudan kudaden da kowanne dan majalisa ke samu don ayyukan mazabu
Dan majalisar Adamawa ya bayyana makudan kudaden da kowanne dan majalisa ke samu don ayyukan mazabu Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro Laori wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Numan/Demsa/Lamurde na jihar Adamawa, ya dora laifin rashin aiwatar da kasafin kudin yadda ya kamata a kan rashin ci gaban tattalin arzikin kasar.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Yola, biyo bayan kaddamar da wasu rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana, cibiyar kwamfuta, zauren gari da dakunan gwaji a Lafia, Demsa, Ndem, Imburu, Bali da Kpasham, mazabar Lamurde/Demsa/ Karamar hukumar Numan.

Rahoton ya kuma kawo cewa Laori ya yi tir da abin da ya bayyana a matsayin gazawar kasafin kudin kasar na shekara-shekara.

A cewarsa, Najeriya ba ta taba cimma fiye da kashi 40 cikin dari na ayyukan kasafin kudi ba.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ba za a biya kudaden da likitoci ke bi ba har sai an gudanar da shirin tantancewa.

Kara karanta wannan

Manyan Jihohin Najeriya 10 Da Suka Fi Yawan Kwararrun Likitoci, Rahoto

Ya kuma ce za a sake nazarin alawus dinsu bayan an magance 'rarrabuwa mai zurfi tsakanin matsayin likitocin da ke yajin aiki'.

Shugaban kasar ya fadi hakan ne yayin wata ganawa da jami'an kungiyar likitocin Najeriya a fadar shugaban kasa, a cewar wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama'a, Garba Shehu ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel