'Yan bindiga sun hallaka fasto a Kaduna, El-Rufai ya yi martani mai zafi

'Yan bindiga sun hallaka fasto a Kaduna, El-Rufai ya yi martani mai zafi

  • A jihar Kaduna, wasu 'yan bindiga sun hallaka wani fasto yayin da suka yi masa dirar mikiya
  • Gwamnatin jihar ta Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ba dangin faston hakuri
  • A halin yanzu, gwamnan jihar ya ba jami'an tsaro umarnin zakulo wadanda suka yi aika-aikan

Kaduna - Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe wani faston cocin Evangelical Church Winning All, Rev. Silas Ali, a karamar hukumar Zangon-Kataf ta jihar Kaduna.

Jaridar Punch ta samu labarin cewa 'yan bindigan su yi wa faston dirar mikiya a ranar Asabar 12 ga watan Satumba.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

Ya ce gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai ya ji ba dadi kan harin sannan ya jajantawa cocin da dangin faston da aka kashe.

Tsageru sun bugi fasto a Kaduna sun hallaka shi, El-Rufai ya yi martani
Taswirar jihar Kaduna | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya ba da umarnin daukar matakin gaggawa

A bangare guda, gwamnan jihar Kaduna ya umarci jami'an tsaro su dauki matakin gaggawa na binciko wadanda suka aikata wannan aika-aika.

A cewar sanarwar da Aruwan ya fitar, wacce muka samo daga jaridar The Guardian:

“Gwamnan ya nuna matukar bacin rai kan rahoton kisan, wanda ya bayyana a matsayin abin tsoro da zalunci. Ya yi addu'o'i don samun nutsuwa ga malamin."

Coci ya ruguje kan masu bauta ana cikin ibada a Taraba, ya hallaka mutane biyu

A wani labarin, Ginin coci ya ruguje a jihar Taraba, inda ya kashe mutane biyu tare da jikkata masu ibada da dama.

Rahoton da muka samu ya ce Cocin na Holy Ghost Church, yana cikin garin Chanchanji ta karamar hukumar Takum ta jihar.

Shugaban karamar hukumar Takum, Shiban Tikari ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Asabar da gidan talabijin na Channels.

Asali: Legit.ng

Online view pixel