2023: Shin Tinubu zai gaji Buhari? Sanannen sanatan arewa ya fede biri har wutsiya kan mulkin karba-karba

2023: Shin Tinubu zai gaji Buhari? Sanannen sanatan arewa ya fede biri har wutsiya kan mulkin karba-karba

  • Sanata Abdullahi Adamu na jihar Nasarawa ya ayyana cewa tsarin karba-karba ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya
  • Tsohon gwamnan, wanda ya bayyana haka a Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba, ya ce za a yi amfani da cancanta don zaɓar ɗan takarar jam'iyyar
  • Adamu ya kuma lura cewa abin fata ne ga mutanen kudu su so fito da wanda zai maye gurbin Shugaba Buhari a 2023

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya gaya wa wadanda ke kira ga mika shugabanci zuwa yankin kudancin ƙasar a 2023 da su binne tunaninsu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Adamu wanda shine sanata mai wakiltar yankin Nasarawa ta yamma a majalisar tarayya ya bayyana mulkin karba-karba a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka fasto a Kaduna, El-Rufai ya yi martani mai zafi

2023: Shin Tinubu zai gaji Buhari? Sanannen sanatan arewa ya fede biri har wutsiya kan mulkin karba-karba Hoto: APC
Sanata Abdullahi Adamu ya ce Kudu ba za ta iya samar da wanda zai maye gurbin Buhari ba Hoto: APC
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon gwamnan na sau biyu ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa tsohon gwamnan na Nasarawa ya ce duk da cewa akwai kiraye-kirayen da ake yi na mika kujarer shugaban kasa ga shiyyar kudu maso gabas, amma babu wani tanadi na tsarin mulki kan hakan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, tunda ra'ayin karba-karba ba ya cikin kundin tsarin mulkin kasar, kowane dan Najeriya da ya cancanta yana da 'yancin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba tare da la’akari da jiharsa ta asali ba.

Ya ce:

“Babu wani wuri a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya da aka ce mu raba kowani kujerar gwamnati zuwa wani yanki. Akwai halin tarayya. Amma ba wai dole ne jam’iyyu su mika mukamin shugaban kasa ga wani yanki ba a lokacin zaɓe.

Kara karanta wannan

Ba tsaro a Najeriya, sai zubar da jini ake, inji Sule Lamido yayin ganawa da Obasanjo

“Ana nazarin kundin tsarin mulki. Idan kuna son takamaiman tanadi cewa a karkatar da mukaman shugaban ƙasa zuwa na karba-karba, sai ku faɗi - sannan ku gaya mana yadda kuke son a raba shi.
“Shin zai kasance daga wannan shiyya zuwa wani ne? Ba za ku iya yin fatan kawai ba, a yanayin da ke da mahimmanci ga ƙasa. Ba za ku iya yin magana game da cancanta da magana kan karba-karba ba. Ba za ku iya ba.”

Adamu ya lura cewa ya kamata jam'iyyar ta tafi da cancanta, inda ya kara da cewa dole ne kowace jam'iyya ta nemi hanyar siyar da kanta ta hanyar da za ta sami irin ƙuri'un da za ta ci zaɓen.

Ya ce:

“Shin muna da irin wannan a cikin tsarin mulkin Amurka? Shin mun fi Amurkawa dimokradiyya ne? Dimokuradiyya ce. Me yasa kuke son canza shi? Son zuciya kawai. Yaya za ku kira shi? Ee, wani yana cewa gabas ba ta da shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin Najeriya na yanzu da za su iya rasa zaben 2023 da dalili

"Na yarda kuma ina tausaya musu amma tsarin mulki ya ce za ka iya zama shugaban kasa ne ta akwatin zabe kawai. Mun kasance muna fada a lokacin zabe cewa dole ne a kirga kowane kuri'a. Don haka, me yasa kuke son yin karba-karba?”

Jiga-jigan APC sama da 30 suna harin kujerar Ministan wutan lantarki da aka tsige

A wani labari na daban, akalla jagororin jam’iyyar APC 32 a jihar Taraba suna neman maye gurbin Saleh Mamman, wanda aka tsige daga mukamin Ministan wuta.

Jaridar Daily Trust tace manyan ‘yan siyasan Kano da Taraba inda Sabo Nanono da Injiniya Saleh Mamman suka fito, suna hangen kujerun Ministocin tarayya.

Ana sa rai shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tura sunayen wadanda za su maye guraben Ministocin da ya kora da zarar ‘yan majalisa sun dawo aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng