Kiwo a fili: A ba mu lokaci mu horar da Fulani makiyaya, Miyetti Allah ta roki Legas
- Kungiyar Miyetti Allah a jihar Legas ta roki gwamnatin jihar da ta daga musu kafa kan dokar hana kiwo sakaka
- Wannan na zuwa ne yayin da jihar Legas ke kokarin sanya dokar hana kiwo sakaka a dokokin jihar
- Kungiyar Miyetti Allah ta ce, za ta koma ta koyar da mambobinta yadda ake kiwo a wuri daya cikin gaggawa
Legas - Sashin kudu maso yammaci na kungiyar makiyaya shanu ta Miyetti Allah (MACBAN) ta ce tana bukatar lokaci don horar da membobinta kan yadda za a daina yawon kiwo a fili, TheCable ta ruwaito.
Maikudi Usman, sakataren shiyyar MACBAN na kudu maso yamma, ya yi rokon ne a ranar Laraba 8 ga watan satumba a wurin taron jin ra'ayin jama'a na dokar hana kiwo a jihar Legas.
Ya ce membobin kungiyar suna bukatar lokaci don a karantar da su kan “yadda za su yi kiwo a wuri daya kuma ba za su taka kasar kowa ba”.
A cewar Usman:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Makiyayanmu ba su saba da kiwon shanu wuri daya ba. Suna tafiya ne daga nan zuwa wani wuri. Idan muka ce za mu ajiye shanu wuri daya, mai shanun ba zai sami kudin ciyar da dabbobin a wuri daya ba.
“Sun riga sun dogara da tafiya daga wannan wuri zuwa wani. Domin a lokacin damina, muna da inda muke sauka, kuma muna da inda muke sauka a rani.
“Muna rokon gwamnatin jihar Legas da ta ba mu lokaci mu je mu fada wa mutanenmu kuma mu horar da su yadda za su yi kiwo a wuri daya kuma kada su fada zuwa kasar kowa.
"Amma kiwo a wuri daya, a yanzu, mutanen mu ba su da ikon yin hakan. Abin da ba ku saba da shi ba, dole ne a koyar da ku. Kuma a hankali, kowa zai fahimta. ”
A ranar Litinin, dokar hana kiwo sakaka ta wuce karatu na biyu a majalisar dokokin jihar Legas.
Idan an zartar da kudirin, Legas za ta shiga cikin wasu jihohi a yankin kudancin kasar da suka sanya dokar hana kiwo sakaka a cikin doka.
Miyetti Allah za ta tura Fulani makiyaya Amurka domin a horar dasu kiwon zamani
Amina Ajayi, Jakadiyar Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hure, kungiyar raya al'adu, ta gabatar da wani shiri mai karfi na horar da Fulani makiyaya akan kiwo na zamani, wanda aka misalta shi da kwatankwacin kiwo a Amurka.
Ajayi ta bayyana hakan ne a cikin jawabinta na karbar mukami biyo bayan nada ta a matsayin Jakadiyar Miyetti Allah a hedikwatar kungiyar ta kasa da ke Uke, Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.
Ta bayyana cewa rukunin farko na masu horaswa da malamai na makarantar Miyetti Allah Cattle Ranch Academy zai yi tafiya zuwa California a kasar Amurka, a farkon 2022, Vanguard ta ruwaito.
Rikici ya barke tsakanin Hausawa 'yan kasuwa da Fulani makiyaya a jihar Delta
A wani labarin, rikici ya barke a yankin Sapele, Karamar Hukumar Sapele ta jihar Delta yayin da ‘yan kasuwa Hausawa da Fulani makiyaya a yankin a ranar Litinin suka yi artabu da kare-jini-biri-jini a Kasuwar Hausa da ke kan hanyar Benin zuwa Warri, Amukpe, a cikin birni.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce akalla mutane goma ne suka samu munanan raunuka a cikin farmakin da ya biyo baya sannan aka garzaya da su asibitoci daban-daban a yankin, in ji rahoton Daily Report Nigeria.
Punch ta ruwaito cewa, an lalata shagunan katako, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa yayin da wasu masu ababen hawa suke tsere suka bar ababen hawansu domin tsira.
Asali: Legit.ng