Sunday Igboho ya ce a mika shi ga Najeriya bai jin tsoron karo da gwamnatin Buhari
- Sunday Igboho ya bayyana cewa, ya kamata a mika shi ga gwamnatin Najeriya don a hukunta shi
- Ya bayyana haka ne a cikin wani faifan sauti da jaridar Punch ta ce ta samu daga majiya mai tushe
- Igboho ya bayyana dalilansa na fadin cewa ya kamata gwamnatin jamhuriyar Benin ta mika shi ga Najeriya
Benin - Wani dan awaren Yarbawa, Sunday Igboho, ya bayyana kwarin gwiwar samun 'yanci idan Jamhuriyar Benin ta dawo dashi hannun gwamnatin Najeriya.
A cikin faifan sautin da jaridar Punch ta samu wanda kuma majiyoyi da yawa suka tabbatar, Igboho ya ce bai damu da a daure shi kamar yadda aka daure Nnamdi Kanu ba.
Ya yi zargin cewa wasu lauyoyi a jamhuriyar Benin sun karbe kudinsa, kuma sun yaudareshi yayin da suka yi watsi dashi a hannun gwamnatin kasar.
Sabon ministan wuta ga 'yan Najeriya: Kada ku yi tsammanin za a samar da wutan lantarki kamar sihiri
Dan awaren yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ya faru ne saboda halin da na tsinci kaina a ciki. Idan na kuduri aniyar yin wani abu, babu wanda zai iya tsayar da ni.
"Sadda na dage cewa ya kamata a canza wurin tsarewar da aka ajiye ni a nan, an tilasta musu su canza shi. Na yarda da kaddara. Ba na jin tsoron kowa. A shirye nake in fuskanci alkali cewa bana jin tsoron sa. Ya kamata yayi duk abinda yake so.
“Idan suna son dawo da ni Najeriya, ya kamata su yi hakan. Akwai Allah a can. Nnamdi Kanu shima yana hannun Najeriya kuma muna yaki iri daya ne. Ban damu ba idan an dawo da ni Najeriya. A shirye nake.
“Ina nan kusan watanni biyu sannan lauyoyi ba su nuna damuwa sosai ba. Ina da manyan lauyoyi a Najeriya wadanda ke girmama ni. Ina da lauyoyi 42 da ke kare ni a Ibadan kuma suna ci gaba da samun nasara.”
A halin yanzu Igboho yana tsare a Jamhuriyar Benin yayin da mutanensa hudu ke tsare a hannun jami'an hukumar tsaro ta farin kaya.
Sahara Reporters ta wallafa sakon sautin da aka ji Sunday Igboho yana bayani a cikin yaren Yarbanci.
Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano
A rahoton da muka kawo muku a watan Yuli, kunji cewa kotun Jamhuriyar Benin da ke zamanta a Kwatano ta tura Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho zuwa gidan yari, The Cable ta ruwaito.
An kammala zaman kotun ne misalin ƙarfe 11.20 na daren ranar Litinin bayan shafe kimanin awanni 13.
Wani majiya daga kotun ta shaidawa The Cable cewa ba za a saki Igboho ba.
"Matsalar mayar da wanda ake zargin da laifi ƙasarsa domin ya fuskanci sharia lamari ne da akwai siyasa sosai a cikinsa."
Majiyar ta kara da cewa Igboho ya yi ta rokon kotun kada ta mayar da shi Nigeria saboda yana tsoron akwai yiwuwar a kashe shi.
Musulunci Ya Haramta: Ban Goyon Bayan Halasta Amfani Da Wiwi, Ƴan Majalisar Kano Ma Basu Goyon Baya, Ganduje
Sheikh Gumi: Tura sojoji su ragargaji 'yan bindiga ba zai magance rashin tsaro ba
A wani labarin, Babban malamin addinin Islama mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi ikirarin cewa farmakin da sojoji ke kaiwa kan 'yan bindiga da ke addabar Arewa maso Yamma ba zai magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta ba.
Malam Gumi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 6 ga watan Satumba ta shafinsa na Facebook, yayin da yake mayar da martani kan nasarorin da sojoji ke samu a kan 'yan bindiga a dazuzzukan Zamfara.
A cikin sanarwar, Gumi ya bayyana yadda gwamnati ke tafka asara wajen kashe kudade don sayen makamai da jiragen yaki kuma babu wani sauyi a yakar 'yan bindiga, wanda a cewarsa, zai durkusar da tattalin arzikin kasar.
Asali: Legit.ng